Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Pantami ya jaddada cewa gaskiya da riƙon amana su ne ginshiƙan shugabanci nagari, yana mai cewa shugabanni su kasance masu tsoron Allah.
Tsohon Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami, ya ce babu wata hukuma mai yaƙi da cin hanci da rashawa da ta taɓa gayyatar sa ko bincikensa a tsawon lokacin da ya yi yana riƙe da muƙamin gwamnati.
Pantami ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Gombe, yayin ƙaddamar da wani kundin littafi da ya ƙunshi bayanan manyan ayyukan ci gaba sama da 241 da ya ce ya aiwatar a jihar.
Ya jaddada cewa gaskiya da riƙon amana su ne ginshiƙan shugabanci nagari, yana mai cewa shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma kula da amanar da aka ɗora musu.
“Da ikon Allah, mun yi shekaru muna aiki a gwamnati, amma babu wata hukuma da ta taɓa gayyatar mu kan zargin cin hanci da rashawa,” in ji shi.
Ya bayyana hakan a matsayin shaida ta yadda ya tafiyar da ayyukansa cikin gaskiya da tsabta, yana mai cewa kiyaye kyakkyawan tarihi a harkokin gwamnati na buƙatar jajircewa da tsoron Allah.
Pantami ya kuma yi kira ga masu riƙe da muƙaman siyasa da masu neman muƙamai da su yi riƙo da gaskiya da amana, tare da tabbatar da cewa ayyukansu za su iya jurewa binciken jama’a.
A cewarsa, ya kamata ’yan Nijeriya su mayar da hankali wajen zaɓen shugabanni masu gaskiya da riƙon amana, domin su ne ginshiƙin ci gaban ƙasa.
Pantami ya riƙe muƙamin minista ne a ƙarƙashin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, daga shekarar 2019 zuwa 2023.
