Fursuna mai haɗari ya tsere daga kurkuku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Gidajen Gyaran (NCoS) reshen Jihar Yobe, ta tabbatar da cewa wani fursuna ya tsere bayan aukuwar wani hatsari da ya rutsa da wata mota mai ɗauke da fursunoni akan hanyar Potiskum zuwa Damaturu.

A cewar jami’in hulɗa da jama’ar hukumar, Abdullahi Adamu, al’amarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Afrilu yayin da ake jigilar fursunoni daga cibiyar tsaro a Potiskum zuwa Damaturu.

A yayin hatsarin, wanda ya auku a lokacin da jami’ai ke ƙoƙarin kula da yanayin da waɗanda abin ya rutsa da su, wani fursuna ya yi amfani da shi wajen tserewa.

An ruwaito cewa, Ɗahiru Mohammed mai shekaru 30 shi ne wanda ya tseren, wanda ɗan ƙauyen Askiwari na Ƙaramar Hukumar Tarmuwa ne.

Tun a ranar 29 ga watan Nuwamban 2024 ne aka tsare shi, wanda ke ɗauke da lambar kurkuku kamar haka: J/1539/24.

Hukumomi sun bayyana shi a matsayin mai haɗarin gaske don haka suka gargaɗi al’umma da kada su ba shi mafaka ko taimaka masa ta kowace fuska, wanda yin hakan babban laifi ne.

Tuni dai aka baza komar kama shi tare da kira ga jama’a da su ruwaito dukkan wani bayani da suka samu akansa domin taimaka wa kama shi.

Haka kuma, an samar da lambobin gaggawa domin aiko da rahoto, tana mai tabbatar wa al’umma cewa ana ƙoƙarin ganin an kamo shi tare da mayar da shi komar hukumar.

By Babaji