2027: ’Yan ADC a Majalisar Wakilai sun buƙaci a binciki shugaban INEC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

’Yan Jam’iyyar ADC a Majalisar Wakilai sun buƙaci a binciki tare da gurfanar da Shugaban Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, bisa zargin nuna son kai da rashin daidaito a matsayinsa na mai sa ido kan zaɓe.

Bayan taronta na farko da ta gudanar a ranar Lahadi, 12 ga Afrilu, 2026, domin duba halin da siyasar ƙasar ke ciki, ƙungiyar ’yan majalisar ta nuna damuwa kan yadda Shugaban INEC ɗin zai iya gudanar da zaɓe na gaskiya, adalci da inganci a 2027, tana mai cewa wasu kalamai da matakan da ya ɗauka sun nuna alamun son zuciya da rashin adalci.

Ta kuma ce ana zargin shugaban ya taba wallafa ra’ayoyin siyasa a shafinsa na ɗ, inda ake cewa ya nuna goyon baya ga jam’iyyar APC mai mulki, tare da wasu rubuce-rubuce da suka janyo ce-ce-ku-ce.

Duk da cewa INEC ta musanta cewa asusun nasa ne, binciken ƙwaƙwaf da wasu majiyoyi suka gudanar sun nuna alamar cewa yana da alaƙa da asusun.

Saboda haka, ƙungiyar ta bukaci a cire Farfesa Amupitan daga mukaminsa tare da gurfanar da shi a gaban ƙuliya, domin kare dimokuraɗiyyar Nijeriya daga durƙusahewa.

Haka kuma, ’yan majalisar sun zargi INEC da ɗaukar wasu matakai da suka saba wa tsarin dimokuraɗiyya, musamman dangane da rikicin shugabanci da ake fama da shi a cikin jam’iyyar ADC.

Sun ce hukumar na ƙoƙarin tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyar ta hanyar amincewa da wani ɓangare na shugabanci da ba sahihi ba.

Sun ƙara da cewa akwai bayanai masu ƙarfi da ke nuna cewa wasu daga cikin jami’an INEC da kuma wasu alƙalai na aiki tare domin juya shari’ar da za a yi ranar 14 ga Afrilu, 2026, dangane da rikicin shugabancin jam’iyyar.

ƙungiyar ta kuma jaddada cewa dokar zaɓe ta 2026 ta haramta wa kotuna tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyun siyasa, tana mai cewa duk wani yunƙuri na yin hakan ya saɓa wa doka.

A sakamakon haka, ta ce ta kammala shirye-shiryen kai ƙara ga Majalisar Shari’a ta ƙasa (NJC), domin a binciki wasu alkalai da ake zargin sun shiga siyasa, tare da yiwuwar ɗaukar matakin ladabtarwa a kansu.

ƙungiyar ta ADC a Majalisar Wakilai ta ce matakin da take ɗauka ya zama dole ne domin kare dimokuraɗiyyar Nijeriya, musamman a daidai lokacin da ake ganin wasu sassa na al’umma sun fara rasa amincewa da hukumomin zaɓe da ɓangaren shari’a.

Ta kuma yi tir da yadda ake zargin wasu ’yan siyasa na bai wa alƙalai kyaututtuka, kamar motoci, tana mai cewa hakan na iya lalata mutunci da ’yancin kai na ɓangaren shari’a.

A ƙarshe, ƙungiyar ta jaddada cewa dole ne INEC ta tabbatar da gaskiya, adalci da kuma amincewar jama’a a ayyukanta, tana mai cewa abin da ke faruwa yanzu na nuna akwai gibi tsakanin manufar hukumar da yadda take aiki a zahiri.

By ukarofi