Tare da BILKISU YUSUF ALI
Mata da dama sukan shiga matsananciyar damuwa yayin da aurensu ya mutu ko da suna da hannu a mutuwar auren nasu ko kuma tsautsayi ya rutsa da su ko ganganci. A yau, Bazawara ba a tunanin ina matsalarta take mene dalili maimakon haka ƙazafi da sharri da kallon banza da tsangwama shi ne zai biyo baya in har ba a yi sa’a da dace ba ana kallo a unguwa sai ta faɗa mummunan yanayi ba mai taimaka mata. Mace ba ita kaɗai ce ke da alhakin riƙe aure ba, hasali ma ita sakin ba a hannunta yake ba, amma ala dole duk gaskiyarta sai ta faɗa fushin dangi da makwabta.
Aure yarjejiniya ce tsakanin ma’aurata bisa sahalewar zukatan juna da amincewa.Duk macen kwarai tana fatan ta ganta cikin gidanta da mijin da ta zaɓa ko iyaye suka zaɓa mata don samun nutsuwa da samun iyali.Akwai dalilai da dama da mata a yau suke fuskata musamman matar da ta taɓa aure ta fito ko dai a sanadiyyar mutuwa ko kuma a sanadin mutuwar aure wanda wannan dalilan ne ke jefa mata cikin taskun rayuwa da rashin kamun kai.
Tarbar fari ta iyaye
Iyaye da dama taryar da suke yi wa ‘yarsu lokacin da suka dawo gida bayan mutuwar aure daga nan suke fara yanke ƙauna da dukkan farin ciki.Ba sa bambance sakin da musabbabinsa sai su ɗauki laifin duniya su jinginawa mace. Za a tsangwame ta a haɗata da ƙannenta suma su ɗora akan tsangwamar iyaye sannan ayyukan gida duk ita ce ke da alhakin yin sa kuma ba ko sannu. Su kuwa ƙanne gwargwadon yadda uka fahimci rashin muhimmancinta a gidan gwargwadon rainin da za su taryeta da shi. Sabulun wanka da wanki da sauran kayan kyalekyalen mata ba me ba ta.Duk wani ‘yanci da take tunanin tana da shi da take gidanta yanzu babu shi da wanne za ta ji?
Yayin da ta zama a hargitse ba nutsuwa a zuci babu a zahiri wanne namijin ne kuma zai kalleta da sunan zai kai gidansa?Tun daga nan an sama mata bizar zama a gida babu ranar tashi. Tarairayarku da ba ta abin da take buƙata dai-dai iko shi ne zai sa ta kauwame ta zama ba ta nema gun kowa kuma ya ba ta damar nutsuwa da zaɓen miji na gari ba tare da gaggawar maza ta tashi ta huta ba inda da dama irin wannan ke haifar da da-na-sani.
ɓarkowar masoya
Barazana ta gaba bayan iyaye yayin zawarci shi ne zawarawa ta kowanne ɓangare su yi tsinke ga sabuwar bazawara. Wannan ɗabi’a ta zama ruwan dare sannan kaso tara daga cikin ɗari na wannan zawarawan ba da gaske auren suke buƙata ba kawai ‘yan rage dare ne da son uwar Inna. In kuma bazawarar ta ɗan taho da sana’a ko abin hannunta za su lallaɓa su cinye da zummar soyayya. Kai in ma sun lura bazawarar mai kamun kanta ce, su su fito mata da maganar aure a yaudareta ta nan. Don haka sabuwar Bazawara sai kin yi takatsantsan don gudun faɗawa samarin shaho.
Rashin Sana’a
Da zarar auren mace ya mutu ta dawo gida wasu iyayen kan ɗauka a yanzu nauyin ‘yarsu da ta dawo gida ba nasu ba ne, don haka buƙatunta ba za a biya mata su ba na yau da kullum. Shawara kada don aurenku ya mutu ku bari zuciyarku ta mutu ba. Yana da kyau Bazawara ta nemi sana’a don tsira daga waɗancan zawarawan da suke yi mata layi da yaudara. In mace tana sana’a tana ɗaukewa kanta buƙatu da dama sannan shi kansa namijin da zai zo auren zai fi himma in ya tarar ba ci-ma-zaune ce ba.
Za mu cigaba a mako mai zuwa In sha Allah.
