Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Wata babbar kotu da ke kan titin Miller a Jihar Kano ta yi watsi da ƙarar da aka shigar kan tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi, Murtala Sule Garo, da wasu mutane biyar bisa zargin cin hanci da rashawa.
Mai Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa ƙarar ba ta cika ƙa’idojin doka ba, musamman kan rashin ingantaccen bincike da kuma batun hurumin shari’a, lamarin da ya sa aka kori ƙarar mai lamba K/133c/2024.
Hukumar ƙarbar ƙorafe-ƙorafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ce ta shigar da ƙarar, tana tuhumar Garo tare da wasu mutane da kamfanoni biyu.
A hukuncin kotun, an jaddada cewa ba za a gurfanar da mutum a kotu ba tare da gudanar da bincike ba, kamar yadda dokar tsarin shari’ar manyan laifuka ta tanada. Haka kuma, kotun ta bayyana cewa PCACC ba ta da hurumin bincike ko shigar da ƙarar da ta shafi cin hanci da rashawa, domin hakan na ƙarƙashin ikon hukumomin tarayya.
Wannan hukunci na zuwa ne a lokacin da ake raɗe-raɗin yiwuwar naɗa Murtala Garo a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna kwamared Abdul Salam a ranar 27 ga watan Maris.
Ana dai tuhumar Murtala Sule Garo ne dai tare da tsohon gwamnan Ganduje da wasu jami’ai da karkatar da kuɗaɗen ƙananan hukumomi, Naira Biliyan 57 na ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano zargin da ke ci gaba da jan hankalin jama’a a jihar.
