Gwamnatin Tarayya ta fara biyan likitoci bashin albashin da suke bi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan likitoci mambobin ƙungiyar NARD kuɗaɗen alawus-alawus da suke bi bashi, waɗanda aka daɗe ana jinkirta biyan su.

Sakataren hulɗa da jama’a na NARD, Abdulmajid Ibrahim, ya tabbatar da hakan ta cikin wani saƙo da aka aike wa mambobinsu, inda ya bayyana cewa za a biya kuɗaɗen ne daga watan 1 zuwa 6.

Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin likitocin sun riga sun fara karɓar kuɗaɗen nasu, har ma sun tabbatar da ganin rasit ɗin biyan.

Haka kuma, an buƙaci waɗanda har yanzu ba su samu nasu ba da su ƙara haƙuri, domin ana ci gaba da aikin biyan kuɗaɗen ga sauran mambobin.

Dakta Abdulmajid ya ƙara da cewa akwai wasu ƙalubale na fasaha da aka fuskanta wajen tura kuɗaɗen, wanda ya janyo jinkiri na kimanin makonni biyu kafin a fara biyan su yadda ya kamata.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙoƙarin inganta walwalar likitoci da kuma ƙarfafa ɓangaren lafiya a faɗin Nijeriya.

By Babaji