
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙasa da sa’o’i 24 da jagorancin ADC tsagin David Mark ke jiran sanin makomarsa daga Kotun Ƙoli, jam’iyyar ta kammala shirye-shirye yayin fara babban taronta na ƙasa a yau Talata a Abuja.
Bincike ya nuna cewa, jam’iyyar ta karɓi babban ɗakin taro a Rainbow Event Centre da ke yankin Garki a babban birnin domin gudanar da taron.
Da fari, wasu rahotanni da ba a tabbatar da sahihancinsu ba sum bayyana cewa an hana wa ADC amfani da filin Eagle Square, zancen d Ministan Abuja Nyesom Wike ya ƙaryata daga bisani.
A baya dai jam’iyyar ta gudanar da taron Majalisar Zartarwarta (NEC) a wajen.
Haka kuma, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ƙi amince wa buƙatar tabbatar da jagorancin su Mark a ADC, idna ta ce ta yi haka ne bisa la’akari da umarnin Kotun Ɗaukaka Ƙara na a girmama doka akan al’amarin.
Akan matakin ne ADC ɓangaren su Mark ya ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙoli wands za a yi hukunci a kai ranar Talata.
