
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Kaduna ta bayar da belin tsohon Gwamnan jihar, Nasir El-Rufai na shari’a mai alaƙa d rashawa da Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) ta shigar akansa, inda kotun ta umarci ya cigaba da zama a hannun hukuma har sai ya cika sharuɗɗan belin.
Mai Shari’a Rilwanu Aikawa ya yi hukuncin a yau Talata bayan ɗage batun daga ranar 1 zuw 14 ga watan Afrilu, 2026, domin yin nazari akan buƙatun ɓangaren masu gurfanarwa da naasu bayar da kariya.
Alƙalin ya bayyana cewa, an bayar da belin ne akan Naira miliyan 200 da kuma mutane biyu da za su tsaya masa.
Kotun ta kuma umarci cewa wajibi ne ga waɗanda za su tsaya masa su miƙa fasfo ɗinsu na ƙasa-da-ƙasa, sannan dole da ne ɗaya daga cikin ya zama jam’i ne na gwamnati mai matsayi na 15 zuwa sama yayin da ɗayan kuma wajibi ne ya sarki da aka sani.
Bugu da ƙari, kotun ta haramta wa El-Rufa’i furta wasu kalamai a bainar jama’a game da shari’ar kuma dole ne ya halarci dukkan zama da kotu ta kira.
Lauyan da ke kare tsohon gwamnan, Ubong Akpan bai samu yin tsokaci ga manema labarai ba bayan zaman bada belin.
To saidai a wani ɓangare kuwa, Babbar Kotun Kaduna ta ɗage ƙorafin bayar da belin tsohon gwamnan akan wata shari’ar da ICPC ta shigar akansa zuwa ranar 21 ga watan Afrilu, 2026, lamarin da ke ƙara tsawaita shari’ar tasa.
