Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh.
Wannan wasiƙa an rubuta ta ne da zuciya ɗaya, da damuwa mai tsanani, da kuma fatan alheri. Ba da ƙiyayya ba, ba da tsinuwa ba, ba da zagi ba. Sai dai da ƙauna, nasiha, tunatarwa da kuma roƙo na gaskiya daga ɗan uwa zuwa ‘yan uwansa. Ina magana ne kai tsaye zuwa gare ku masu tuƙin ganganci – masu karya doka, masu sa rayuwar kansu da ta jama’a cikin hatsari a kullum.
Direbobin motoci masu zaman kansu, masu kabu-kabu, musamman ’yan J5, Golf da Hiace. Masu adaidaita sahu da masu babur, musamman matasa. Da farko, ku sani cewa babu wanda aka haifa domin ya mutu a titi, sai dai idan iftila’i ta afku. Babu wanda aka haifa domin a kwashe shi daga titi zuwa kan gadon asibiti saboda rashin kula da dokoki. Babu uwar da ta haifi ɗa domin ya zama tarihi saboda ganganci. Babu matar da ta auri miji domin ta zama bazawara kuma uwar marayu saboda rashin haƙuri. Amma abin takaici, kusan kowace rana muna wayar gari da labarin mutuwar matasa, raunuka masu tsanani da kuma hawaye na iyaye, duk sakamakon tuƙi ba tare da hankali ba.
Ku tambayi kanku: ina nake gudu na je? Ina zan kai da nake gudun wuce kima? Idan na mutu yau, me zan bar wa iyayena? Me zan bar wa ‘ya’yana? Me zan bar wa matata? Me zan bar wa al’ummata? Shin ganganci ya fi rayuwata daraja ne?
Ku dubi hanyoyinmu. Cike suke da hawaye, kuwwa da jini. Hanyoyin nan sun shaida yadda ake ganin matasa bisa babur cikin annushuwa da safe, amma a dawo da su cikin jini da tsakar dare. Sun shaida yadda ake ɗora gawa a motar asibiti ana kuka. Ba wai saboda ba su yi addu’a ba, sai dai saboda ganganci ya riga ya yanke hukunci.
Ku saurari gaskiya: yawancin waɗanda ke mutuwa a hazurra ba su da laifi. Mata masu juna biyu, yara ƙanana, tsofaffi, ɗalibai, ma’aikata. Su ba su zaɓi su shiga hatsari ba, amma gangancin wani ne ke kashe su. Dukkanmu masu laifi ne idan muka bar wannan abu yana faruwa ba tare da mun tsaya tsayin daka ba.
Masu tuƙin ganganci, ku sani cewa hikima ba ta cikin gudu. Jarumta ba ta cikin karya doka. Duk wanda yake tuƙi da ganganci ba jarumi ba ne, bai ƙware ba, bai fi kowa ba. A’a, mutum ne da ke wasa da rayuwarsa da ta wasu.
Ku tuna da doka. Ba wai an rubuta dokoki don wahalar da ku ba ne, sai dai don kare ku. Dokar hana gudu ta wuce kima, dokar hana talleke layi a wuraren wutar bada hannu, dokar hana bin hanya ɗaya (one-way), dokar guje wa shan barasa yayin tuƙi – duk kariya ce gare ku kafin al’umma. Idan kuka karya doka, ba wai gwamnati kuka cutar ba, kanku ne kuke cutarwa, iyayenku kuke kashewa sannu a hankali da damuwa.
Na san wasu daga cikinku talauci ke ingiza su, wasu rashin aiki, wasu ɗaukar fasinja ne kawai domin neman abincin rana. Amma talauci bai ba ka lasisin kashe rai ba. Neman halal bai ba ka izinin karya doka ba. Rayuwa da wahala ba hujja ba ce ta halakar da kai da wasu. Akwai bambanci tsakanin “zafin nama” da “ganganci”.
Ku daina wannan tunani na cewa “idan lokacin mutuwarka ta yi, ƙaddara ce.” ƙaddara gaskiya ce, amma sakaci laifi ne. Ba duk abin da ya faru sakamakon ƙaddara ba ne, wasu sakamakon zaɓin mutum ne. Idan ka sha barasa ka hau mota ka bige mutum ka ce ƙaddara ce, ka zalunci ƙaddara. Idan ka yi gudu ba tare da la’akari da jama’a ba sai haɗari ya faru, ba ƙaddara ba ce kawai, akwai sakacin da ya jawo.
Ku dubi iyayenku. Wasu sun sayar da gona, wasu sun sayar da shanu, wasu sun ci bashi ne don su saya muku ababen hawa. Sun yi haka da fata cewa za ku taimake su a gobe, ba don su binne ku yau ba. Duk lokacin da kuka hau mota ko babur da ganganci, ku sani kuna jefa zuciyar iyayenku cikin wuta ne.
Ku dubi matanku. Wasu matan da ke zaman zawarci a yau ba tsofaffi ba ne, matasa ne. Mijinsu ya fita da safe a kan babur, bai dawo da rai ba. Yara suka barsu suna tambaya: “Ina Baba?” Me za su ce? Me za su faɗa wa yara idan kuka zama tarihi saboda ganganci?
Ku dubi al’umma. Hanyoyi masu lafiya su ne tushen cigaban ƙasa. Idan muka maida hanyoyi maƙabartu, ta yaya kasuwanci zai bunƙasa? Ta yaya makarantu za su yi aiki lafiya? Ta yaya mata da yara za su yi tafiya ba tare da tsoro ba?
Idan kuna cikin fushi, kada ku hau mota. Idan kun sha barasa ko wasu kayan shaye-shaye, kada ku yi tuƙi. Idan kuna da gajiya sosai, ku huta. Idan kun kasa jure wa bin doka, ku ajiye tuƙi gaba ɗaya. Babu wani aiki da ya fi rai daraja.
Ina kuma kira ga abokai, don Allah idan kuka ga abokin ku yana tuƙin ganganci, ku tsawata masa. Kada ku riƙa masa dariya. Kada ku ce “shi jarumi ne, ai wane akwai gangaci, cikin ba’a.” A’a, ku ce masa “kai daina irin wannan abu mara kyau.” Ku hana shi, ku tsawata masa, ku kai rahoto idan ya zama dole. Wani lokaci tsawatarwa sau ɗaya tana ceton rayuka da dama.
Ina kira ga iyaye: kada ku riƙa ba wa ‘ya’yanku abin hawa ba tare da tsauraran sharuɗɗa ba. Kada ku ce “ai yaro ne.” Yaro na iya kashe kansa da wasu. Ku riƙa bibiyarsu, ku san irin yadda suke tuƙi, ku hukunta su idan sun saɓa.
Ina kira ga malamai da shugabanni: ku riƙa jan kunne a kan mimbari, a kasuwa, a taro. Ku faɗa wa jama’a cewa ganganci haramun ne, laifi ne, zalunci ne. Rayuwa ba wasa ba ce.
Allah Ya kiyaye ku, Ya kiyaye iyayenku, Ya kiyaye fasinjojinku, Ya kiyaye al’umma baki ɗaya. Allah Ya sa mu dace, mu gyara, mu zama dalilin ceton rayuka ba halakarsu ba.
Wannan shi ne roƙona gare ku – daga zuciya zuwa zuciya. Na gode.
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD, Karamin Edita, Blueprint Manhaja. 07066778190.
