Zuwa ga masu ɓata aikin ɗan sanda: Gargaɗi da kira zuwa ga gyara

Spread the love

Aikin ɗan sanda wata babbar amana ce da aka ɗora wa wasu daga cikin ‘yan ƙasa domin kare rayuka da dukiyoyi, tare da tabbatar da doka da oda a cikin al’umma. Wannan aiki ba kawai sana’a ba ce, illa wata hidima ce ga ƙasa da jama’a, wadda ke buƙatar gaskiya, riƙon amana da tsoron Allah. Sai dai abin takaici, a yau ana ci gaba da samun wasu ‘yan sanda da suka karkace daga wannan turba, suna taɓa mutuncin aikin ta hanyoyi marasa dacewa, lamarin da ke jawo rashin amincewar jama’a ga rundunar baki ɗaya.

A wasu sassan ƙasar nan, musamman a manyan hanyoyi da titunan cikin gari, ana yawan ganin yadda wasu jami’an tsaro ke tare hanya, suna tsayar da masu ababen hawa—musamman masu babura da adaidaita sahu—ba tare da wani dalili na doka ba. Maimakon bincike na gaskiya ko tabbatar da tsaro, sai a fake da duba lamba a juya aikin zuwa wata hanya ta neman kuɗi ta tilas. Sau da yawa, ana tilasta wa waɗannan matasa masu neman abin rufin kai su bayar da kuɗi domin a bar su su wuce, ko da kuwa ba su aikata wani laifi ba.

Wannan ɗabi’a ba kawai tauye mutuncin aikin ɗan sanda ba ne, har ma tana ƙara dagula al’amuran tattalin arziki da zamantakewa. Matasa da dama na dogaro da sana’ar babur ko adaidaita sahu domin ciyar da iyalansu, amma irin wannan cin zarafi yana rage musu ƙarfi da kwarin gwiwa. A maimakon su ga jami’an tsaro a matsayin masu kare su, sai su fara kallonsu a matsayin masu cutar da su—abin da ke kawo giɓi mai haɗari tsakanin jama’a da masu tsaron su.

Bugu da ƙari, irin wannan hali yana buɗe ƙofa ga manyan laifuka, domin wasu taɓa-gari su kan shiga rigar ‘yan sanda su riƙa lwace baburan mutane. Idan jami’in tsaro ya mayar da hankali kan karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, to yaya zai iya mai da hankali wajen gano masu aikata manyan laifuka? Ta haka ne ake rasa sahihancin aiki, kuma ake barin masu aikata laifi su ci gaba da cin karen su ba babbaka.

Sai dai duk da wannan ƙalubale, akwai haske a gaba. A ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, an fara ganin ƙoƙari na gaske na gyaran rundunar. Rahotanni da dama sun nuna yadda ya nuna tsattsauran ra’ayi kan yaƙi da cin hanci da rashawa da cin zarafin al’umma a cikin rundunar, tare da ɗaukar matakan ladabtarwa kan duk wanda aka kama da aikata ba daidai ba.

Salon jagorancinsa ya nuna cewa ya saka ƙafa ɗaya wajen tsaftace harkokin ‘yan sanda, yana ƙoƙarin dawo da martabar aikin da kuma gina amincewar jama’a. Wannan yunƙuri abin a yaba ne, domin gyaran irin wannan babbar hukuma ba abu ne mai sauƙi ba. Yana buƙatar jajircewa, gaskiya da kuma haɗin kan kowa—daga manyan jami’ai har zuwa ƙananan ma’aikata.

Duk da haka, gyara ba zai yi tasiri ba sai idan kowane jami’i ya fahimci cewa shi ne wakilin doka a idon jama’a. Dole ne ‘yan sanda su guji duk wata ɗabi’a da za ta ɓata musu suna, su kuma rungumi kyawawan halaye da suka dace da aikinsu. Hakazalika, ya zama wajibi a ƙarfafa tsarin sa ido da ladabtarwa domin tabbatar da cewa duk wanda ya saɓa wa doka ya fuskanci hukunci ba tare da nuna son kai ba.

Haka kuma, al’umma ma tana da rawar da za ta taka. Ya kamata jama’a su daina bai wa jami’an tsaro cin hanci, ko da kuwa ana matsa musu. Rahoton duk wani cin zarafi ko rashin gaskiya ga hukumomin da suka dace zai taimaka wajen kawo gyara. Idan aka haɗa ƙoƙarin gwamnati, rundunar ‘yan sanda da kuma jama’a, akwai yiwuwar dawo da martabar aikin.

A ƙarshe, aikin ɗan sanda ginshiƙi ne na zaman lafiya da ci gaban kowace ƙasa. Idan aka gyara shi, al’umma za ta amfana; idan kuma aka bar shi cikin lalacewa, to sakamakon zai shafi kowa. Saboda haka, wannan kira ne ga duk masu ɓata aikin ɗan sanda da su tuba, su koma kan turba madaidaiciya, su tuna da amanar da aka ɗora musu.

Lokaci ya yi da za a dawo da martabar aikin ɗan sanda a Nijeriya—domin amfanin kowa da kowa.

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. Karamin Edita, Blueprint Manhaja. 07066778190.

By ukarofi