Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya raba kayan fara sana’a ga matasa 1,169 da suka kammala shirin horaswa kan kanikanci ƙarƙashin shirin Mechatronics Apprenticeship Support Programme (MASP).
Shiri ne wanda hukumar bunƙasa kasuwanci ta Jihar Katsina (KASEDA) ta gudanar tare da haɗin gwiwar Nigerian Automobile Technicians Association (NATA), na da nufin bai wa matasa ƙwarewar sana’o’in zamani domin dogaro da kai.
Da yake jawabi a wajen taron,
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatinsa na bunƙasa sana’o’i da samar da ayyukan yi ga matasa.
“Wannan shiri wata muhimmiyar hanya ce ta rage rashin aikin yi da kuma ƙarfafa matasa su zama masu dogaro da kansu,” in ji Gwamnan.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa sana’o’i da fasahohin zamani, musamman a fannin gyaran motoci na zamani (mechatronics), wanda ke buƙatar sabbin dabaru da ilimi.
Gwamnan ya jaddada cewa bayar da starter packs ga waɗanda suka kammala horon zai taimaka musu fara sana’a kai tsaye, tare da ƙarfafa tattalin arziki a matakin ƙasa.
Ya shawarci waɗanda suka amfana da shirin da su yi amfani da ilimin da suka samu cikin gaskiya da jajircewa, domin su zama abin alfahari ga al’umma.
A nasa ɓangaren, shugabannin KASEDA da NATA sun bayyana cewa shirin ya samu nasara sosai, inda ya bai wa matasa dubban dama na koyon sana’a tare da samun kayan aiki don fara rayuwa mai ɗorewa.
Shirin MASP na daga cikin manufofin gwamnatin jihar na “Building Your Future”, wanda ke mai da hankali kan bunƙasa matasa, ƙarfafa sana’o’i da haɓaka tattalin arziki.
