Daga ALI ABUBAKAR SADIK
Jiya wani kanina ya yi posting cewa “Nan da shekaru biliyan 5 Duniya za ta tashi in ji masana”. To, a gaskiyar lamari ba haka abin ya ke ba. Abinda masana Ilimin sararin samaniya ke hasashe shine cewa Rana, wadda ita ce ginshikin wanzuwar Duniya, a yanzu ta kai rabin shekarunta. Wato an haifi wannan Rana tamu kimanin shekaru biliyan 5 da su ka wuce, kuma za ta iya sake kai wasu shekaru biliyan 5 din kafin ta mutu. Masana sun gane haka ne sakamakon nazarin ragowar makamashin nukiliya da ke ci a Rana, wato tamkar dai ace ka zuba kwalbar kananzir guda a fitila. Kuma wannan kananzir ya na kai awa goma kafin ya kare. Duk inda ya ci na awa biyar, ka san saura wasu awanni biyar ke nan kafin ya kone.
Sakamakon fahimtar yadda taurari, kamar halittu a Doron Duniya su ke, to, ana haihuwar su, su balaga su tsufa sannan su mutu. A yanzu Ranar mu na ganiyar balagar ta, nan da wasu biliyoyin shekaru zata tsufa kafin ta mutu. Idan ta mutu, kuma Duniya na nan a wannan lokaci, wajibi ne yayin mutuwar tata su mutu tare da duniyar mu. Domin a lokacin da Rana ta kone makamashin ta, za ta yi wata irin bindiga (supernoɓa) da zai watso wuta ta lakume duniyoyi hudu makusantanta (Mercury, Venus, Earth da Mars). Kafin abinda ya rage nata ya dunkulule a tsakiyarta, ta yi wata irin takurewa waje guda wadda ko dai ta haifar da Neutron star, wato dunkulalliyar Rana mara haske ko kuma idan nauyinta ya kai ta zama Black Hole, wato bakar tauraruwa wadda ba a iya gani saboda karfin maganadisunta zai sa ko haske ba zai iya fita daga cikinta ba.
Wannan shine sakamakon nazarin masana yadda taurari irin Rana ke mutuwa a sammai kuma ake hasashen ita ma ranarmu haka zata kare. To, amma mu sani cewa ita duniyar mu, zata iya kaiwa wannan lokaci amma kuma ba lallai ba ne. Domin a yau, idan Allah ya so duniyar nan tamu na iya karewa idan wani daga cikin manyan duwatsun sammai (meteorites) ya fado kan wannan Duniya ta mu, zai iya wargaza ta nan take. A baya, tarihin wannan Duniya ya bamu cikakkun shaidu na irin wadannan manyan duwatsun da su ka fado Duniya su ka halaka ilahirin halittu na wancan lokaci. Misali na baya-bayannan shine wani dutsen da ya fado a Yucatan peninsula da ke kasar Meɗico, shekaru miliyan 66 da su ka gabata wanda ya hallaka kakannin kadangare (Dinosaurs) da kusan kashi 75% na duk halittun wancan zamani.
Wannan dutsen, fadinsa bai wuce kilomita 15 ba, amma da ya daki Doron kasa a Yucatan, ya haifar da wani wagegen rami (Crater) mai fadin daga Kano zuwa Kaduna (200km). Karfinsa ya kai na bom din nukiliya guda biliyan daya. Ya watsa kura da ke dauke da tokar Sulphur wadda ta turnuke sararin samaniya ya haifar da yanayin dare a sassan Duniya na watanni, baya ga haifar da igiyar tsunami da ta kai tsawon kilomita daya da rabi, tare da haifar da wutar daji a sassa da dama. Tokar Sulphur ta kashe manyan dabbobi da suka rage a Doron kasa da tsayar da rayuwar akasarin tsirrai wanda ya haifar da mutuwar kananan halittu da su ka dogara da tsirrai.
Wannan fa sakamakon dutse guda ne da bai fi fadin kilomita 15 ba. A hoto na kasa, za ku ga wani Dan digo wanda ke nuna inda duniyar mu ke zaune a yanzu, kuma duwatsu sun mata zobe. Wannan zobe na duwatsu shi ake kira da asteroid belt. Masana na hasashen cewa wata Duniya ce wadda karfin maganadisun Jupiter ne ya wargaza ta a farko-farkon samuwar rukunin tauraron mu, wato Rana (solar system). Duk da wannan Duniya ta wargaje sai karfin maganadisun Jupiter ya rike buraguzan basu warwatse ba, su ka ci gaba da dawafi (orbit) tsakanin Jupiter da Mars. Sannan sai maganadisun Rana shi kuma ya dawwamar da wannan dawafi na su a wurin. Amma duk da haka, lokaci-lokaci, wani cikin wadannan buraguzai na iya tserewa ya nufi wani wajen, kamar yadda waccan dutse ya subuto ya fado Duniya a Yucatan peninsula shekaru miliyan 66 da su ka gabata. A cikin wadannan duwatsu, mafi girmansu da muka gano zuwa yanzu shine dutsen Ceres, mai fadin kilomita 940 (kamar daga Kano zuwa Lagos) da kuma ɓesta, mai fadin kilomita 524 (kamar daga Kano zuwa Sokoto).
Idan wancan da ya fado Duniya shekaru miliyan 66 da su ka wuce da bai fi kilomita 15 ba, me kake tsammani Ida Ceres (940km) ko ɓesta (524km) su ka fado Duniya a yau? Allah ya alƙawarta mana cewa lallai ne a ƙarshe wannan Duniya. ƙ89:21 “A aha! Idan aka nike kasa, nikewa.”
Tabbas a duk lokacin da irin wannan duwatsu su ka subuto daga cikin wannan gungun duwatsu (asteroid belt) su ka fado kan Duniya, tabbas za su nike kasa nikewa tamkar gari (vaporize). Ya kai dan uwa, zauna cikin shirin haduwa da Allah kawai, domin a kowane lokaci ya na iya zare maka Rai, ita kuma duniyar kanta a kowane lokaci ta na cikin zullumin wannan barazana daga makwabtan mu a wannan rukuni na tauraron mu.
Jummu’a mubarak!!!
Malam Ali Sadiƙ manazarci ne a Kano
