Neman alfarma ga masu kaɗa ƙuri’a da masu yin kamfen na zaɓen 2027

Spread the love

Daga UNCLE LARABI

Don Allah a daure, duk wanda za a zaɓa a yi yarjejeniya da shi akan ba ma son ya yi mana komai tsahon shekaru huɗu na farkon mulkinsa sai waɗannan abubuwan guda uku kacal. Sune kamar haka;

1. Samar da tsaro a ƙasarmu Nijeriya.

2. Samar da wutar lantarki.

3. Samar da hanyoyin sufuri na ƙasa masu inganci (titina). 

Idan ya amince zai samar da iyakar waɗannan abubuwan ukun kacal, mu amince mu ba shi ƙuri’unmu bisa amana. Kada mu ruɗu da yawan ƙarya da alƙawuran da duk wani ɗan takara zai yi mana na cewar zai yi mana ayyuka sama da guda ɗari, amma ƙarshe ya zo ko ɗaya ya kasa yi.

Nijeriya muna da ɗimbim ayyukan da ya kamata a ce tuni an wuce wajen, musamman wutar lantarki. Ina Jin da gangan duk wani shugaba yake kin tsaya wa tsayin daka ya ga ya samar da ita, don amfanin al’umma. 

Don Allah a zaɓen 2027 mai zuwa kada mu bi son zuciya ko bara-gurbi. Mu tsaya mu duba cancanta mu zaɓa. MU kuma tabbatar da mun ƙulla wannan yarjejeniyar da duk wanda zai shugabancen mu.

Mun gaji da matsalar rashin tsaro. Ina tuna lokacin da nake iya hawa motar haya da dare tun daga Kano zuwa Lagos ba tare da fargabar za a tsare motarmu a sace mu ba. Ina kuma iya tuna lokacin da nake hawa mota da dare tun daga Kano har Birnin Kebbi ba tare da tsoro ko fargabar ‘bandits’ ko ‘kidnappers’ ba. Ina iya tuna lokacin da nake hawa mota tun daga Kano har Maiduguri ba tare da fargabar Boko Haram za su saka bom motarmu ta tarwatse ba. 

Wannan duk yanzu ya kau. An gadar mana da fargaba da tsoro. 

Matsalar rashin kyawun titina kuwa wannan abin ya ƙazanta ta yadda kusan kullum sai an yi asarar rayuka da yawa a manyan hanyoyinmu. 

Matsalar wutar lantarki kuwa wannan abin ya yi munin da ba a iya samun wuta ko da tsakar dare ne ya tsahon awa shida. Ko da a irin lokacin bikin sallah ko Kirsimeti ko Ista ko maulidi ne yanzu duk ba a samu. Da an kawo sai a ɗauke. Idan ka na son ka ga haske ko kashe iska sai dai ka haɗa sola. 

Allah ya kawo mana shugabannin da za su ji tausayinmu su gyara mana ƙasarmu Nijeriya. 

Uncle Larabi, wato Abdullahi Jibril Larabi Dankantoma, marubuci ne a Kano – Nijeriya. Za a iya samun sa a 08065418892

Alhamis, 9 ga Afrilu, 2026

By ukarofi