Addini daban siyasa daban

Spread the love

Assalamu alaikum, da fatan mun yi sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin.

Akwai wani abinda ke faruwa a ƙasar nan, mutane suna gwama lamarin siyasa da addini. Suna kamfen da sunan da sunan addini, wuce wani musulmi, wane ba Musulmi ba. Wasu har ɗaukar siyasa suke a matsayin jihadi.

Da masu addini Kirista da Musulmai za su gane, da kuma ’yan ƙabilanci za su gane, da basu riƙa damuwa da wannan siyasa ba. Domin addini daban siyasa daban, musamman ma a ƙasar Nijeriya.

Idan Addini ka ke so, ka koma gefe, domin babu ruwan Siyasa da Addini, idan kuma siyasa ka ke so to ka bar maganan addini. Ka yi siyasa, idan ka gama ka dawo addini. Kar ka ce zaka zaɓi wane saboda addini, ko za ka ki shi saboda addini. Addini daban Kuma siyasa daban.

Idan addini ɗaya ne ya ke da siyasa, gaya min wane jam’iyya Sahabbai su ke goyon bayan shi? Ko wane jam’iya Yesu Almasih yana tare da su?

ƙabilanci, wahala kawai ku ke sha, Na’am, dama dama ƙabilanci za a iya cewa tana da ɗan alaƙa da siyasa, amman ban da Nijeriya. Domin duk wanda ya ke yin siyasa saboda ƙabilanci a Nijeriya yana cikin wahala.

Ya kai mai hankali, ka yi tunani ka gani, shin idan ka zage da sunan cewa kana son wani saboda addini ko ƙabikanci, to wallahi kana ruwa.

Kowanne ’yan siyasan mu, aljihun su suke gyarawa, fatan kowa miyarsa ta yi kyau to mene ne na ɓata lokacin ka da cewa sai wane Musulmi zan zaɓa bayan kuma kasan ƙasar ba ƙasar Musulunci ba?

Haka kaima Kirista, kar ka shiga siyasa saboda addini, domin ƙasar ba ƙasar Kiristanci ba ne. Kasa ce ta Dimukraɗiyya, ƙasa ce ta kowa da kowa, idan Addini ka ke so to ka bar siyasa ka koma addini, idan kuma siyasa ka ke kar kace kana addini.

Idan an kashe ka a siyasa, kar ka yi zaton saboda addini aka kashe ka. Idan ka yi jihadi a siyasa, fasadi ka yi ba jihadi ba. Jihadi yana addini, fasadi yana siyasa.

Allah ka bamu shugaba na gari, tare da kuma kawo ƙarshen ƙabilanci da ke tsaƙaninmu ’yan Nijeriya. Ameen

Saƙo daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected].

By ukarofi