Rahoto

Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Daga FARFESA AHMAD MURTALA MANSUR Ci gaba daga makon jiya. iii- Bitcoin ba shi da zubi da tsari irin na katinan da ake ajiye kuɗaɗe a cikinsu kamar katina irin su ɓisa Card, Master Card da sauransu. Saboda su wadannan katina suna da wasu kamfanoni da suke kula da su. Amma tsarin Bitcoin ya tsani duk wata hulda da za a ginata a kan wani kamfani a tsakiya tsakanin mutane! 8- Bisa irin bayanai da aka kawo a karkashin lamba ta 5 na matsaloli guda tara, da bayanan da suka zo a karkashin lamba ta 7, duka wadannan suna nuna…
Read More
Gwamnan Katsina ya bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga ƙungiyar ‘yan wasan guragu

Gwamnan Katsina ya bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga ƙungiyar ‘yan wasan guragu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bai wa ’yan wasa da jami’an da suka wakilci jihar a gasar National Para Games karo na uku da aka kammala a Abuja kyautar Naira miliyan 10. Gwamnan ya sanar da bayar da kyautar ne lokacin da ya karɓi tawagar a gidan gwamnati da ke Katsina, bayan rawar da suka taka inda jihar ta zo a matsayi na 13 a faɗin ƙasa. Da yake gabatar da tawagar, kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Injiniya Surajo Yazid Abukur, ya bayyana cewa jihar Katsina ta fafata a fannoni daban-daban…
Read More
BON ta karrama Gwamnan Zamfara da lambar yabo a fannin ababen more rayuwa

BON ta karrama Gwamnan Zamfara da lambar yabo a fannin ababen more rayuwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Hukumar kula da kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (BON), ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da lambar yabo ta “Gwamnan Shekara a Fannin Ababen More Rayuwa,” sakamakon gagarumin ci gaban da gwamnatinsa ta samu musamman a shirin sabunta birane a faɗin jihar. An miƙa wa gwamnan wannan babbar karramawa ne a yayin bugu na biyu na taron BON da aka gudanar a cibiyar taro ta NAF Conference Centre da ke birnin Abuja, inda manyan mutane daga sassa daban-daban suka halarta. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya…
Read More
Ɗan Sarkin Daura ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar ɗan majalisar wakilai

Ɗan Sarkin Daura ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar ɗan majalisar wakilai

Daga UMAR GARBA a Katsina Muhammad Ɗaha Umar Faruk, babban ɗan Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar majalisar tarayya ta Ɓaure/Zango a babban zaɓen 2027. Faruk, wanda ke riƙe da sarautar gargajiya ta Ɗanburam Daura, ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara don amsa kiraye-kirayen da jama'a ke yi masa na neman ya wakilce su a majalisar tarayya. "Ina so in sanar da dukkan magoya bayana cewa ni, Muhammad Ɗaha Faruk, na yanke shawarar amsa kiransu," in ji shi. "Na amince na tsaya takarar kujerar majalisar tarayya don wakiltar mazaɓar tarayya ta Ɓaure/Zango…
Read More
Karin aure a wurin malam bahaushe

Karin aure a wurin malam bahaushe

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jarida mai farin jini, Manhaja. Allah ya sa mu amfani juna, amin. A yau darasin namu mai tsauri ne, don haka zan yi iya mai yuwa don ganin bai kasance rubutun da za a yi wa mummunar fahimta ba. Kafin mu kai ga darasin namu, bari mu waiwayi abinda littafi mai tsarki Al'ƙur'ani ya faɗa game da auren mace fiye da ɗaya. Allah mazaukakin Sarki Ya faɗa a cikin littafi mai tsarki, "Ku aura daga abinda ya yi muku daɗi na daga mataye, biyu, ko uku, ko…
Read More
Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari'a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane. Lokacin da Ahmed Baba ya rayu: An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu…
Read More
William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Laberiya kasa ce ta 'yantattun bayi, wadda aka gina da musguna wa 'yan ƙasar lokacin da aka zaɓi William Tubman a matsayin shugaban ƙasa. Bayan haɗa kan mutane, ya shirya ƙasar bisa tsarin ci-gaba wanda bai samu ba. An haifi William ɓacanarat Shadrach Tubman ranar 29 ga watan Nuwamba 1895. Ya fito daga yankin kudu maso gabashin Laberiya, daga garin da ake kira Harper na gundumar Maryland. Sunan wuraren ya yi kama da na Amurka, saboda Jamhuriyar Laberiya ta ayyana samun 'yanci daga Amirka a shekarar 1947 da 'yantattun bayi suka yi, waɗanda suka dawo daga…
Read More
Kar ɗan ƙetare ya ƙetaro da zuga!

Kar ɗan ƙetare ya ƙetaro da zuga!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Haƙiƙa harin da ya auku a Jos jihar Filato inda a ka samu asarar rayuka abun takaici ne ainun don yadda a ka samu wani lokaci a na samun sauƙin irin wannan yanayi. Mafi zama abun baƙin ciki shi ne muhawarar da ta biyo bayan wannan hari inda wasu ke neman cusa batun addini ko ƙabilanci a fitinar ko farmakin. Ba dabi’a ba ce mai kyau masu yayata bayanai musamman a yanar gizo su yi wuf su rubuta abun da su ka ga dama ba takatsantsan gabanin jami’an tsaro ko waɗanda su ka cancanta su gudanar…
Read More
Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Bitcoin: Tarihinsa, amfaninsa, matsalolinsa da hukuncin mu’amala da shi a Musulinci

Daga FARFESA AHMAD MURTALA MANSUR Ci gaba daga makon jiya. 6- A halin yanzu duk da waɗannan matsaloli, amma akwai ƙasashen da suka huwace amfani da Bitcoin kamar ƙasashe irin su Jamus, Ingila, Sweden, South Korea, Kuwait, Oman, Jordon, da sauransu. Wasu manyan kamfanonin manhajar kwafiyoyutoci da kafofin sadarwa irinsu Microsoft da Google da Yahoo duk sun karbi amfani da wannan kwandala ta Bitcoin. Haka nan wasu gidajen sayar da abinci da otel-otel duka sun yarda a biyasu ta hanyar amfani da ita. Takai ana sayan wasu tikitin na hawa jirgin sama da kudin Bitcoin. Sannan kuma an sami wasu…
Read More
Kalubalen bazuwar makamai a hannun jama’a 

Kalubalen bazuwar makamai a hannun jama’a 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba mun sha ganin rahotannin da ake bayyanawa a kafafen watsa labarai, dangane da yadda jami'an tsaro ke kama mutane masu safarar ƙananan makamai, da suka haɗa da bindigogi da harsasai. Na san za ka yi mamaki jin cewa daga cikin irin mutanen da ake kamawa har da mata, kuma a cikin su za ka samu akwai Musulmi da Kirista.  Kamar yadda wani mawaƙi a kafar sadarwa ke cewa, 'ɗan iska ba shi da kama!' To, babu shakka haka ne, mugun mutum ba shi da kama, domin kuwa a…
Read More