Kalubalen bazuwar makamai a hannun jama’a 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba mun sha ganin rahotannin da ake bayyanawa a kafafen watsa labarai, dangane da yadda jami’an tsaro ke kama mutane masu safarar ƙananan makamai, da suka haɗa da bindigogi da harsasai. Na san za ka yi mamaki jin cewa daga cikin irin mutanen da ake kamawa har da mata, kuma a cikin su za ka samu akwai Musulmi da Kirista. 

Kamar yadda wani mawaƙi a kafar sadarwa ke cewa, ‘ɗan iska ba shi da kama!’ To, babu shakka haka ne, mugun mutum ba shi da kama, domin kuwa a cikin kowacce al’umma ana samun nagari da mugu. 

A yayin da Nijeriya ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro a sassa daban-daban, wata matsala da take zama babbar damuwa ga jami’an tsaro ita ce ta yadda mugaye ke fakewa cikin jama’a nagari suna aikata ɓarna. A cikin unguwanni da ƙauyukanmu muna sane da ɓatagari da ke tada zaune tsaye ko masu aikin ƙera makamai da safarar su, amma ana ganin ba komai ba ne, saboda ana ganin illar abin da suke yi ba su take shafa ba. Da irin haka ne aka ƙyanƙyashe mayaƙan Boko Haram, da ’yan bindiga masu kai hare-hare a ƙauyuka, da masu satar mutane.

Sakamakon ƙaruwar hare-haren ta’addanci da rikice-rikicen ƙabilanci da na addini, musamman a sassan arewacin Nijeriya, kasuwar masu safarar makamai ta buɗe, ta yadda ake shigo da makamai daga maƙwaftan ƙasashe, ta cikin tashoshin mota, ta ruwa da ma ta ɓarauniyar hanya. Wasu a kama, wasu kuma su wuce ba tare da jami’an tsaro sun gano su ba. Wannan ya sa matsalar tsaro da ta’addanci ke ci gaba da ta’azzara. 

Bazuwar makamai a hannun jama’a ta zama babban abin barazana ga zaman lafiyar al’umma ba ma a Nijeriya kaɗai ba har ma da duniya bakiɗaya. Wannan lamarin ya jefa rayuwar mutane da dama cikin haɗari, ya kuma lalata zamantakewar al’umma, da cigaban ƙasa. Bincike ya nuna cewa, daga cikin jihohin da aka fi samun masu safarar makamai a arewacin Nijeriya sun haɗa da Sakkwato, Zamfara, Kaduna, Filato, Taraba da Borno, saboda yawan hare-haren ‘yan bindiga da safarar makamai a yankunan da kuma ta iyakokin ƙasar nan. Wani rahoto ya bayyana Jihar Sakkwato a matsayin jihar da ta fi sauran jihohi wajen kama masu safarar makamai, kamar a watan Janairu 2026 inda jami’an tsaro suka cafke mutane biyu da ke kai makamai ga tantiran ‘yan bindiga a Jihar Zamfara daga Jamhuriyar Nijar. Wannan nasara ta kasance saboda rahotannin sirri da ake samu daga jama’a da bincike mai zurfi.

ƙungiyar Amnesty International da Small Arms Survey sun gudanar da bincike na musamman a shekarar 2023 inda suka gano akwai makamai sama da biliyan ɗaya a hannun mutane fararen hula a duniya, kuma a arewacin Afirka da yammacin ta, adadin makaman da suke yawo a hannun jama’a ya ƙaru a kashi 20 cikin ɗari a cikin shekaru 10 da suka wuce. A shekarun da suka gabata, hare-hare sun ƙaru saboda kwararar makamai zuwa cikin ƙasar nan daga iyakoki. Misali, a shekarar 2025, rahotanni sun nuna cewa satar shanu da fashi sun faɗaɗa daga rikicin makiyaya da manoma, wanda ya zama sanadin rashin tsaro a yankunan karkara.

A nan Nijeriya, jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Bauchi, Zamfara, Sakkwato, Katsina, Kaduna, Binuwai, Nasarawa, Neja da Filato da kuma Kano a baya-bayan nan sun yi ta fama da hare-haren ’yan bindiga tare da salwantar rayuka da dukiyoyi masu ɗimbin yawa. A dalilin haka, an samu koma bayan tattalin arziki, lalacewar zamantakewa, da ƙaruwar rikice-rikice nan da can, wanda ya haifar da mummunan rashin jituwa a tsakanin al’ummomin da suka daɗe suna rayuwa tare.

Misali, a Jihar Filato rikicin ƙabilanci da na addini ya haifar da mummunar rashin yarda da yawan tashe-tashen hankula a tsakanin Musulmi da Kirista a jihar. Wannan ya sa an samu rabuwar wuraren zama, kasuwanci da makarantu, da yawan ƙyamar juna. Za a iya cewa, hakan na da nasaba da yadda ake yawan samun rahotannin kama mutane masu safarar makamai a cikin jihar, ko masu ƙera makamai a lunguna daban-daban. 

A yayin da nake wannan rubutu garin Jos, babban birnin Jihar Filato na cikin alhini da fargaba, sakamakon ɓarkewar wani rikici da ya biyo bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wata anguwa ta Kirista, wanda ya haifar da asarar rayuka kusan 30, ciki har da wasu Musulmi da ke kasuwanci a wajen da masu wucewa. Awoyi kaɗan bayan harin Jos, an kuma rawaito cewa wasu ’yan bindiga sun kai wani harin wajen wani taron biki a Kagarko ta Jihar Kaduna. Nan ma an samu asarar rayuka da kuma sace mutane da dama.

Waɗannan hare-hare duk suna nuni ne da yadda makamai suka yi yawa a hannun jama’a fararen hula, don haka kashe-kashe suka yawaita. Barazanar ɗaukar fansa a tsakanin matasa ita ma ta ƙaru, har wasu na cewa a ba su dama su goge raini, saboda gadarar suna da makamai a hannu. Wani rahoto ya bayyana yadda a shekara 2024, jami’an sojojin Nijeriya sun samu nasarar kama ‘yan bindiga 11,623, tare da ƙwatar makamai 8,216 da harsasai 211,459 daga hannun ‘yan ta’adda. Wannan ya haɗa har da kama wasu masu safarar makamai daga jihohin Borno zuwa Taraba.

Wani rahoton Hukumar Kula da Aikin ɗansanda ta ƙasa ya nuna cewa a shekara 2025, akwai makamai sama da 5,000 a hannun jama’a cikin jihohin Arewa, wanda hakan ke ƙara tabbatar da halin rayuwar da jama’a a yankin ke zaune cikin fargaba da tsoro. Yadda jama’a ke tsoron fita kasuwanci da gonakinsu saboda tsoron hari, ya haifar da ƙarancin abinci da tsadarsa a kasuwanni, da kashi 40 cikin ɗari a wasu yankuna, kuma ya haifar da ƙaruwar fatara da talauci.

A sakamakon fitintinun da ke faruwa a birane da ƙauyukan Arewa, mutane suna jin tsoron fita gona ko kasuwanci, kamar yadda ake gani a jihohin Zamfara, Katsina, Borno da Yobe da kuma Filato saboda yadda ’yan ta’adda ke barazana ga rayukan jama’a, da amfani da makamai don hana manoma zuwa gonaki, da yadda dokar hanazirga-zirga take takura mutane a gida da hana su fita kasuwanci, ko kuma tsoron za a kawo musu hari. 

Lallai ne gwamnati da haɗin gwiwar ƙungiyoyin sakai na gida da na waje su shiryawa jama’a bita kuma su ƙarfafa su wajen koya musu ilimi kan haɗarin mallakar makamai ba da izini ba. A kuma ƙarfafa haɗin gwiwar jami’an tsaro da farar hula wajen sa ido da bayar da bayanan sirri kan bazuwar makamai a cikin unguwanni da wuraren zaman jama’a. Dole ne mu haɗa kai don yaƙi da wannan mummunar halayya ta mallakar makamai ba izini da ke lalata rayuwarmu. Gwamnati ta yi amfani da bayanan sirri da jama’a ke bayarwa, don fatattakar ƙungiyoyin ’yan ta’adda tare da masu rura wutar rikicin ƙabilanci.

By ukarofi