Rikicin ADC: An yi wa shugaban INEC barazana da takardarsa ta murabus – Farfesa Odinkalu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fitaccen masanin shari’a, Farfesa Chidi Anselm Odinkalu, ya soki Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) bisa matakin da ta ɗauka na fassara hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara a shari’ar da ke tsakanin jiga-jigan jam’iyyar ADC, Sanata David Mark da Nafiu Bala Gombe da sauransu.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin ɗ, Odinkalu ya zargi shugabannin INEC, da shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kuma Kotun ɗaukaka ƙara da Babbar Kotun Tarayya da hannu a wani taro da ya ce ya haifar da sanarwar da INEC ta fitar, wadda ke ɗauke da fassarar hukuncin kotu.

Ya bayyana cewa, “Ba aikin INEC ba ne ta fassara hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara. Idan akwai ruɗani, ya kamata ta koma kotun domin neman ƙarin bayani cikin gaskiya da bin doka.”

Odinkalu ya ƙara da cewa, yana da sahihan bayanai da ke nuna cewa akwai wata takardar murabus da aka riga aka sanya hannu daga Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, wadda aka ce sharaɗi ne kafin naɗinsa.

Ya yi zargin cewa an yi amfani da barazanar fitar da takardar domin tilasta masa fitar da sanarwar.

A cewarsa, halin da ake ciki a yanzu na nuna cewa ƙasar na fuskantar wani mawuyacin yanayi gabanin zaɓen 2027, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su fahimci girman abin da ke tafe.

A nata ɓangaren, jam’iyyar ADC ta yi watsi da fassarar da INEC ta yi, tana mai zargin cewa an tilasta wa hukumar yin hakan sakamakon matsin lamba daga Gwamnatin Tarayya.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi ya sanya wa hannu, ADC ta ce duk da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na raunana jam’iyyun adawa, tana nuna tsoro ne sakamakon ƙaruwar karɓuwar jam’iyyar a idon jama’a.

Sanarwar ta bayyana cewa matsayar INEC ta cika da saɓani kuma ba ta dace da gaskiyar lamarin ba, tana mai cewa hukumar ta zaɓi goyon bayan gwamnati maimakon kare muradun ’yan ƙasa. Jam’iyyar ta kuma ce tana nazarin matakan da za ta ɗauka nan gaba, tare da kira ga mambobinta da su kasance masu juriya.

A baya dai, INEC ta sanar da cire sunayen Sanata David Mark da Rauf Aregbesola daga jerin shugabannin ADC a shafinta na yanar gizo, inda ta ce ba za ta amince da kowanne ɓangare na jam’iyyar ba har sai an kammala shari’ar da ke gaban Babbar Kotun Tarayya.

Haka kuma, hukumar ta dakatar da sa ido kan duk wani babban taro ko zaɓe na cikin gida da kowanne ɓangare na jam’iyyar zai gudanar, har sai an yanke hukunci na ƙarshe kan rikicin shugabanci da ya addabi jam’iyyar.

Wannan lamari ya biyo bayan rikicin shugabanci da kuma hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara da ya ƙara rikitar da al’amura, lamarin da ke ci gaba da jawo muhawara a fagen siyasar ƙasar nan.

By ukarofi