Bayan jan layi da Kwankwaso, Gwamnan Kano na neman haɗa kai da Shekarau don faɗaɗa dabarun siyasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya fara tattaunawa akan shawarwarin siyasa da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau a wani yanayi na ƙarfafa matsayinsa yayin tunkarar zaɓen 2027.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake sauye-sauyen tafiyar siyasa a Kano, wadda ɗaya ce daga cikin jihohin Nijeriya da harkar siyasa ke da gagarumin tasiri acikin al’umma.

Fasalin siyasa a jihar ya sauya ne bayan da Gwamna Abba ya jingine tafiyar uban tafiyar siyasarsa kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso tare da ficewa a jam’iyyar NNPP da koma wa mai mulki APC, matakin da ake gani a matsayin abin da zai ƙarfafa salon siyasarsa.

A wani ɓangare kuwa. Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar tare da koma wa ADC da ke cigaba da samun jiga-jigan ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na Nijeriya acikinta.

Haka ma Nasir Gawuna, wanda ya kara da Abba a zaɓen gwamna na jihar da ya gabata, ya bar APC domin koma wa ADC.

Tuni dai Gwamna Abba ya yi wata ganawar sirri da Shekarau a Abuja tare da Shugaba APC na Kano Umar Haruna Doguwa, a wani salo da majiyoyi na kusa suka bayyana a matsayin yunƙurin lallashin tsohon gwamnan na ya koma APC.

Wata majiya ta kusa da Shekarau ta tabbatar da ganawar, inda ta ce an yi ta ne da manufar ƙarfafa tafiyar siyasa a Kano da ka iya haifar da sabuwar tafiya a jihar.

By Babaji