Gwamnan Katsina ya bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga ƙungiyar ‘yan wasan guragu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya bai wa ’yan wasa da jami’an da suka wakilci jihar a gasar National Para Games karo na uku da aka kammala a Abuja kyautar Naira miliyan 10.

Gwamnan ya sanar da bayar da kyautar ne lokacin da ya karɓi tawagar a gidan gwamnati da ke Katsina, bayan rawar da suka taka inda jihar ta zo a matsayi na 13 a faɗin ƙasa.

Da yake gabatar da tawagar, kwamishinan matasa da wasanni na jihar, Injiniya Surajo Yazid Abukur, ya bayyana cewa jihar Katsina ta fafata a fannoni daban-daban da suka haɗa da ƙwallon kafa da gasar harbi, tseren keke,guje guje da tsalle tsalle da gwajin nauyi.

Ya yaba da yadda ’yan wasan suka nuna ƙwarewa, jajircewa da ɗabi’a nagari a duk tsawon gasar.

Ya kuma bayyana cewa matashin ɗan wasan tseren keken guragu mai shekaru 18, Hamza Abdulmumini, an gayyace shi zuwa sansanin ƙasa domin wakiltar Nijeriya a gasar All African Games mai zuwa. Haka kuma, an zaɓi ’yan wasan ƙwallon ƙafa su biyar daga Katsina cikin tawagar ƙasa.

Kwamishinan ya danganta wannan nasara da goyon baya da zuba jari da gwamnatin Gwamna Raɗɗa ke yi a harkar wasanni, tare da roƙon a samar da ƙarin kyaututtuka, horas da ƙarin masu horaswa da jami’an gudanarwa domin ƙarfafa fannin wasanni a jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Raɗɗa ya taya ’yan wasan murna bisa yadda suka ɗaga martabar Katsina, tare da sake jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa harkar wasanni a matsayin hanya ta bunƙasa matasa, gano baiwa da inganta haɗin kai. Ya buƙace su da su ci gaba da jajircewa tare da tabbatar musu da cikakken goyon bayan gwamnati.

By ukarofi