Kar ɗan ƙetare ya ƙetaro da zuga!

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haƙiƙa harin da ya auku a Jos jihar Filato inda a ka samu asarar rayuka abun takaici ne ainun don yadda a ka samu wani lokaci a na samun sauƙin irin wannan yanayi. Mafi zama abun baƙin ciki shi ne muhawarar da ta biyo bayan wannan hari inda wasu ke neman cusa batun addini ko ƙabilanci a fitinar ko farmakin. Ba dabi’a ba ce mai kyau masu yayata bayanai musamman a yanar gizo su yi wuf su rubuta abun da su ka ga dama ba takatsantsan gabanin jami’an tsaro ko waɗanda su ka cancanta su gudanar da bincike don fito da gaskiya.

An dawo da hada-hada a Jos babban birnin jihar Filato bayan kammalar wa’adin dokar ta-ɓaci ta hana yawo dare da rana a Larabar da ta gabata.

Birnin mai hada-hadar sana’o’i da harkokin kasuwanci ya fara murmurewa daga fitinar wani hari a Anguwar Rukuba inda a ka samu asarar rayuka.

Wasu marar sa kishin ƙasa sun shammaci jami’an tsaro inda su ka so tada sabuwar fitina bayan dawo da zirga-zirga.

Aƙalla dai an sake samun asarar rai na mutum ɗaya a fitinar da dama ka iya rikiɗewa zuwa faɗan addini ko ƙabilanci. ɗaukar duk wani matakin rigakafin hana bazuwar rikicin zuwa sauran sassa na da muhimmanci. A irin wannan yanayin ne ƙaddara kan iya aukawa matafiya da za su iya faɗawa tarkon masu huce haushi kan waɗanda ba ruwansu.

Da alamu jami’an tsaro za su ƙara bazuwa dukkan sassan da lamarin ya shafa da duk inda a ke jin a ka iya samun keta doka da oda. Haƙiƙa akwai yankunan da har yanzu ba a samun Musulmi ko kirista su shiga hankali kwance don yadda a ka samu shekaru da dama a na samun fitina da hakan kan yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a.

Shugaba Tinubu zai sauka a Jos ɗin don jajantawa kafin wucewa wasu jihohin don ƙaddamar da ayyuka.

Shugaban dai tun farko ya yi Allah wadai da hare-haren a Filato da kuma jihar Kaduna.

Masu azancin zance kan ce idan mai zarmiya ya samu rana sai ya yi shanya kuma a nan Nijeriya inda wasu ke fakewa da ‘yancin fadar ra’ayi wajen ingiza mutane su dau makamai don yaki a doron addini da ƙabilanci. Haba irin wannan na ƙetare Aleɗ Barbir in a Mali, nan nan Afurka ta yamma ya zagi matashin sojan nan ai da ya gane kuskurensa. A Nijeriya ne yaro ƙarami zai hau soshiyal midiya ya zagi Shehu Mujaddadi, ya zagi gwamnan jiharsu ya zundumawa hatta shugaban ƙasa ashar amma ya kwana lafiya. In ma a wani lokacin jami’ai su ka riƙe wani don bincike sai mutane su yi ca su na cewa #freewane-wane# ba a ma ko maganar wane laifi ya aikata. Ya zama wajibi hukumomi su nuna Nijeriya ƙasa ce mai doka da oda duk wanda ya wuce gona da iri a ja kunnensa ko a ladabtar da shi don zama gargaɗi ga sauran masu karambani su shiga taitayinsu. Idan an gwada misali kan daya ko biyu to wasu masu niyyar kauce hanya za su janye su natsu.

Irin kalmomin da matashin nan na ketare ke furtawa da ma faifan da ya ɗauka a Rukuba jim kaɗan bayan samun fitina na nuna tamkar dama ya na nan makale a daf da wajen don jiran miyagun su kai farmaki shi kuma ya ɗau faifan bidiyon har da zargin mai girma shugaban ƙasa babban kwamandan askarawa cewa ya na zaune a fadar Aso a na samun irin wannan matsala. Shin aikinsa ne furta wannan kalami da isar da wannan sako? Ina masu masaukinsa su ka shiga da barinsa ya yi wo gaba don raina hukumomin tsaron kasarmu? Haƙiƙa akwai buƙatar gudanar da bincike. Ai na ce mu ku akwai zargin ‘yan bazata ke sa a dau faya-fayan bidiyon nan don tunzura jama’a, sai ka ga sun rubuta “…yanzu haka za mu zauna sai an karar da mu..?” kalmomi ne na buga kugen yaƙin basasa.

Wannan abun da ya faru ya kara tabbatarwa jama’a cewa duk ta’addancin nan ɗaukar nauyinsa a ke yi da zummar ruguza tasirin siyasa, tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Arewa. Masu basaja da rigar ƙabilancin nan na aiki ne da umurnin miyagun nan na ciki da abokan burminsu na ketare. Wani shakiyyi kwanaki ya rubuta wai ai ba Chinedu ko Chibuzor ne ke kai mu su hari ba amma bai damu da su waye ke samar da makamai da miyagun kwayoyi ga mutanen da ya ke kalawa fitjnar ba. Kazalika sam-sam bai ma taba zuwa inda a ke tashin hankalin ba, ya na can gidan barasarsa ya na sheke aya riƙe da wayar salula. Kama daga masu ruruta fitinar ƙabilanci da yaƙin addini a soshiyal midiya zuwa kan ‘yan ta’addan nan na nan yammacin Arewa da ma can gabashi na karɓar umurni ne daga iyayen gidan ‘yan bazata. An yi walƙiya mun ga miyagun nan tsirara. Me ya saura illa a cafke su don mu samu zaman lafiya mai ɗorewa a yi noma a yi kiwo lafiya ba kare bin damo.

Duk wasu hotuna da bidiyo da su ka fito daga akasin da ya auku a Anguwan Rukuba a Jos, ba wanda ya kai na Bayammen nan Aleɗ da ya yi wuf ya dau faifai da ke nuna ba mamaki hatta wadanda su ka kai farmakin ma na nan a wajen ko ba su yi tafiya mai tazara ta komawa ramin ƙurarsu ba. Shin waye ya ɗau bidiyon a kamara ? don faifan ba na ɗaukar kai da kai ba ne. Hakan ya nuna akwai tawaga ta musamman da ke tare da wannan Bayammen madugun ‘yan bazata a lokacin da akasin ya auku. Don tsananin raini da shaƙiyanci, Bayammen nan ya kalli kamara ya ci zarafin maigitma shugaban ƙasa har da cewa zai yi nadama. Tsakani da Allah kun taɓa ganin wani Bayamme ya ɓullo a inda a ka tare matafiya a ka yanka su ya na nuna juyayi da kushe ko da shugaban ƙaramar hukuma ne?. Haƙiƙa akwai tambayar da mu ke ganin mukarrabin Bayammen nan wato Reɓerend Ezekiel Dacomo ya kamata ya fito ya amsa tun da mun ga shi ke zagawa da shi su na furta kalamai na ingiza mabiya. Bayammen nan da ke nuna tallafi ya kawo ga wadanda a ke kai wa hari, shin wa kuma ya ba shi hurumin magana a madadin ‘yan Nijeriya hart a kai ga mizanin neman aibata shugaban ƙasa? Ai Amurka na tutiya da doka da oda kuma ko shugaban Amurka yau ya aikata ba daidai ba, a kan kai shi ƙara kotu don ba wanda a zahiri ya fi ƙarfin doka. Indai haka ne tsarin dimokraɗiyyar Yammawa na makirci to sam ba wata riba ga ƙasashenmu na Afurka.

Wallahi duk kalamai a faya-fayan bidiyo da na gani na yawon wannan Bayammen madugun Bazatawa a Binuwai da Filato duk na kira ne ga ɗaukar makamai a shiga dauki ba daɗi wato yaƙin addini. Shin wa zai ci riba tsakanin Musulmi da Kirista in an zubar da jini? Hakika ba wata riba sai karin bakin ciki, zaman ɗar-ɗar na fargabar ramuwar gayya da karayar tattalin arziki. Shekarun baya ai garin Jos na daya daga birane mafi tasiri a Arewa da mutane kan so su tattara kayansu su koma can, amma da wasu matasa da a ka yaudara da kiyayyar ba gaira ba dalili wacce ba ta cikin kowane littafi mai tsarki, mutane kan yi ajiyar zuciya in sun biyo Filato sun fice ba a tare su an yanka su ba. 

KAMMALAWA

Yawaitar fitinar ya sa hatta tattalin arzkin Jos da sauran sassan jihar ya ja da baya nesa ba kusa. Kawai wasu matasa da ke bin zugar Bazatawa irin su Aleɗ kan sheke matafiya sai kuma gobe su ɗauka za su fito kan titi su na sayar da kaya, mutane su tsaya su saya! Tabbas wasu ma sun daina bin jihar tun da su ka samu labarin Janar na soja ma an tare shi ba tare da ya yiwa kowa laifi ba, don bambancin addini an kashe shi da turbuɗe gawarsa a ramin jeka-na-yi-ka inda a ka tunkuɗa motarsa wani kududdufi. Bara-baran nan ma wasu matafiya daga Zaria don su na tambayar hanya, haka a ka zubar da jininsu. Ba a ga Aleɗ ko masu masaukinsa na yin bidiyo don nuna damuwa ba. Ga ɗaliban Sheikh Dahiru Bauchi ma da har dutse wani ya ɗauka bayan make daya daga cikinsu, ya ribza ma sa a ka ya tarwatsa kwanyarsa. Duk an aika mutanen nan lahira don ƙiyayyar addini da masu ayyuka irin na Bayammen nan ke rurutawa. Mu na kyautata zaton hukuma za ta hanzarta takawa mutumin nan da abokan tafiyarsa birki.

Duk yadda Reverend Ezekiel Dachomo ke magana da babbar murya amma a gabansa Aleɗ ke cewa mabiya ikilisiya ba su da murya a Nijeriya, haba waye ne marar nazari a cikin masu sauraro?

Ina amfani da wannan dama wajen kira ga Musulmi da Kirista na Arewa kar mu bar masu kambama zaman doya da manja su rikito babbar fitina don kar a yi sunan wani ɗan fashi Terwase Akwaza da ya ci zamaninsa a Binuwai ya na ta’addanci kafin dubunsa ya cika.

By ukarofi