Daga FARFESA AHMAD MURTALA MANSUR
Ci gaba daga makon jiya.
iii- Bitcoin ba shi da zubi da tsari irin na katinan da ake ajiye kuɗaɗe a cikinsu kamar katina irin su ɓisa Card, Master Card da sauransu. Saboda su wadannan katina suna da wasu kamfanoni da suke kula da su. Amma tsarin Bitcoin ya tsani duk wata hulda da za a ginata a kan wani kamfani a tsakiya tsakanin mutane!
8- Bisa irin bayanai da aka kawo a karkashin lamba ta 5 na matsaloli guda tara, da bayanan da suka zo a karkashin lamba ta 7, duka wadannan suna nuna cewa wannan harka ta Bitcoin tana kunshe da abubuwa da yawa da suka isa a ce ‘Haram’ ce bisa dokokin Shari’a. Ga bayanin dailan haramcin a dunkule:
i- Riba: Riba tana shiga hadahadar Bitcoin musaman ta fuskoki biyu:
Fuska ta daya ana sayar da kwandalar bitcoin da bitcoin da fifiko da karin wata a kan wata, wanda yake riba ne. Sannan a wasu lokutan ana samun jinkiri, ba a samun hannu-da-hannu ko da ‘bayarwa ta ma’ana’ ce a wajen canji da ake yi tare da sauran kudade.
Fuska ta biyu kuma, kamfanonin da suke saye da sayar da Bitcoin a kasuwannin kudi, wato (brokers), suna karbar kudin mutan kamar N 5,000, sai su ranta masa wasu kudaden masu yawa kamar N 50,000 a kan wadancan. Daga nan sai su zubasu a sayen ‘share’. Idan kudi suka habaka, aka ci riba, sai su bawa mutum iya kason da ya dace da kudinsa, su kuma su rike ragowar a matsayin (commission). Wannan shi ake kira da ‘Leɓerage’, wanda yake haramun ne ta fuskoki da yawa. Daga ciki dai Akwai bashi da riba da aka yi da sunan wanda ya sa kudi tun farko. Sannan kuma ya yarda da ya taimaka a ci riba. Wannan duka haram ne.
Idan kuma an fadi, to duk kudin mutum (N 5,000) din baki daya sun salwanta, ya yi asararsu! Wannan bangaren ya shiga tsarin caca zindim!
ii- An gina Manhajar Bitcoin a kan tsarin caca. Shi ma wannan zai iya zamowa ta fuskoki da yawa, musamman gida biyu.
Fusaka ta daya ita ce wadda ta gabata a misalin da aka fada a lamabar sama cewa idan mutum ya sa kudi misali (N 5,000), shi kuma ‘broker’ ya kara, sai a ka sami asara, to kudin mutum sun nutse baki daya, ba zai sami komai ba.
Fuska ta biyu kuma kamfanomin da suke fafutukar samo ‘coin’ din ta hanyar ‘mining’ suna kashe dimbin kudade su zunduma cikin zabari tare da sauran masu nema, a karshe sai guda daya ne zai iya samu a cikin minti goma. Sauran ba wanda zai sami wani abu. Kowane irin abu suka kashe na dukiya ya tafi a banza.
iii- Cin dukiyar mutane ba-gaira-ba-dalili: Kula da dukiyoyin mutane da kiyayesu daga salwanta yana daga cikin manufofin Shari’a. Akwai sauki sosai ta hanyar Bitcoin a sami damar cin dukiyar mutane ba tare da wata wahala ba. Saboda yadda farashin Bitcoin yake gwauran tashi a dan kankanin lokaci, yana huwacewa wasu su azurta da kudaden mutane ba gaira-ba-dalil. Sannan kuma ya sauka adan lokaci, ta yadda wasu zasu yi gagarumar asara. Wannan yana bada tsoro har ana tunanin cewa akwai wasu a boye masu ci da gumin sauran mutane! Tsarin hawa da saukar Bitcoin ya wuce tsarin yadda aka san cinikayyar canji a kasuwar duniya ta yadda hawa da saukar ba wani mai yawa ba ne, amma ba ya ninninka ba. Misali Bitcoin ya taba ninkawa har sau dari uku a 2017 sannan kuma ya ruguzo! Wannan yana nuna Bitcoin ba kudi ba ne da za a dogara da shi. Wasu daga cikin msana tattalin arziki suna cewa, ‘hauhawar Bitcoin kamar tashin kumfa take’ (bubble), nan da nan zata sauka a dawo kasa!
Imamu Ibnu Kayyim ya fayyace wasu ka’idoji da za a fahimci yadda tsarin kudi yake a Musulunci. Ya ce, “Dirhami da Dinare kudade ne na kadarori da kayan sayarwa. Abin da ake nufi da kudi shi ne ya zamo ma’auni, wanda za a rika kimanta kimar sauran dukiya da shi. Don haka ne dole ya zamo mai iyaka, aka san gwargwadon yadda zai kai ya kawo, ba ya tashi samai sosai, ko ya fadi kasa warwas! Domin idan kudi yana tashi , yana sauka kamar wata kadara, ba zai zamo man kudi da za a rika la’akari da shi wajen kimar kayan sayarwa ba. Sai duk su zamo kadara ne, tare da cewa bukatar mutane zuwa ga tsuran kudi wanda za su rika la’akari da shi dangane da kayan sayarwa, wannan bukata ce ta larura, da ta shafi kowa. Shi kuwa tabbatar da wannan sai da wani farashi da za a san kimar abubuwa da shi. Shi ma wannan sai da wani tsarin kudi da za rika yiwa abubuwa kima ta kima da shi, wanda zai zarce a kan hali daya, ba wai shi ya zamo ana yi masa kima da wani abin ba, saboda ya zamo kadara da zai tashi ya sauka. Yin haka kuwa zai bata tsarin mu’ammalar mutane, sabani ya shiga tsakaninsu, cutuwa ta tsananta a cikinsu” -(I’lamul Muwakki’in An Rabbil Alamin na Ibnul Kayyim:2/157).
Wannan bayani ne mai matukar karfi, tare da cewa Ibnul Kayyim ya yi shi ne bisa duba da la’akari da tsarin kudi tuntuni. Sai dai a zahiri bayani ne kamar yau aka yi shi da ya shafi irin gararin da Bitcoin yake son jefa mutane a ciki. Domin a halin yanzu mu’amallar da ake yi da Bitcoin din tare da cewa na yi masa kirarin cewa kudi ne, amma mu’amallar irin wadda Ibnul Kayyim ya fada tana so ta mayar da shi kamar kadara/haja ba kudi ba !!
iɓ- Garari: Akwai garari a ciki saboda idan an tura kudade ba za a iya shan kansu ba a dawo da su ba, idan misalign an fasa cinikin. Sai dai in wancan bangaren wanda ba a san kowaye ba, ya tausaya ya dawo da su. Sannan wanda aka yi ciniki da shi zai iya cinyewa mutane kudadensu ba tare da an kaishi wurin hukuma ta hukunta shi ba. Don haka wanda yake wannan mu’amalla ya shirya karbar mummunar asara da abokan mu’amallar ba za su san mai yake ciki ba ma ballantana su yi tunanin tausaya masa ba!
ɓ- Jahala: A cikin huldar Bitcoin akwai rashin sanin yadda wasu abubuwan suke gudana da yawa. Domin ba komai ne a fayyace ba. Hatta wanda mutum yake haulda da su, mutum bai gama fahimtar su waye ba, ta yaya suka tara kudadensu, shin yana taimakawa marasa gaskiya ko kuwa? Da dai sauran irin wadannan tambayoyi masu wahalar amsuwa. Muhimmi dai ana so a gina ciki ba bu jahiltar abin da cikin ya kunsa. Imamu Ibnul Arabi Al-maliki yana cewa, “Malaman wannan al’umma sun hadu a kan cewa cinikayya bata kulluwa sai ga abin da aka sani, daga wanda aka sani, da abin da aka sani, ta kowace irin fuska wadda za a iya samun sanayar”-(Al-Kabas Shurhul Muwadda na Ibnul Arabi Al-Maliki:2/786-803).
9- Kasancewar duk ma’anoni guda uku da suke ruguza cinik wato, riba, garari da algush, sun hadu a wannan mu’amalla ta Bitcoin, ya wajaba ga wanda yake yin hadahada da Bitcoin da ya dakata, ya daina. Ya sayar da abin da ya tara a lalitarsa sannan ya kwashe uwar kudinsa, ragowar kuma ya badasu sadaka ko ya sa su a wani aikin alheri da al’umma zata amfana da su bakidaya. Wanna saboda Allah Madaukakin Sarki ya ce, “In kun tuba, to sai ku rke uwar kudinku, ba ku zalinci kowa ba, kuma ba a zalinceku ba”-(Bakara2:279).
10- Mu’amallar Bitcoin tana da dan rikitarwa. Abubuwa da yawa ba su bayyana ba a cikinta sai daga baya. Wannan ya sa malamai sun yi dan yi sabani wajen fitar mata da hukunci, musaman a shekara ta 2017, a lokacin da lamarin Bitcoin ya burinkasa, mutane suka fadaka da irin yadda zata kawo musu kudi suna kwance, ba wata wahala.
Malamai a daidaikunsu da kuma Majalisu sun zauna a lokuta daba-daban don su tabbatar da hukuncin wannan mu’amalla. Daga cikin wadanda suka tattauna mas’alar, suka kuma tabbatar da cewa ta sabawa Shari’ar Musulunci akwai Majalisar Malamai ta Kasar Turkiyya (Darul Ift’it Trukiyyah, 29/11/2017: https//goo/gl/Kɓƙoyr), da Misra (Darul Ifta’il Misriyyah, 28/12/2017: https//goo/gl/WTMpdu); da Falasdinu (Majlisul Ifta’ Al-Filisdiniyya: https//goo/gl/TEMmlu).
Haka nan, akwai taron karawa-juna-ilimi da aka yi a Doha ta kasar ƙatar (4th Doha Islamic Finance Conference) a January, 2017 M. sun tattauna irin kudaden da ake hulda da su ta hanyar internet kawai. Masu taron, wadanda suka hada da Dr. Abdussattar Abu Ghudda-Allah ya yi asa rahama- da Dr. Aliyu Kardagi da sauran masana a fagen tsarin tattalin arziki na Musulunci, sun tabbatar da cewa irin wadannan sababbin cinikayya suna da rikitarwa da hadarin gaske, musaman da yake ba wani nassi da ya zo a kansu. Amma fitar da hukunci ga irin wadannan mas’aloli ba zai gagari masana Fikihu ba a cikin malaman Musulunci.
Bayan haka manyan malamai sun dada zama a karkashin Majma’ul Fikihil Islami Addauli (International Islamic Fiƙh Academy) a farkon shekara 1441 H./2019, a inda suka tattauna sosai a kan dabi’ar wannan mu’amalla.
11- Akwai wasu abubuwa wadanda idan Bitcoin da sauran huldodi masu kama da shi suka cikasu za a iya la’akari da su a janye harmcin da yake kansu a yanzu kamar yadda Sheikh Aliyu Kardagi ya bada shawara. Wadannan abubuwa sun hada da:
i- Gwamnati ta dauki Bitcoin a matsayin kudi. Don haka sai sami wata kasa ta yarda da tsarin Bitcoin da makamantanta, ta yadda Babban Bankin kasar zai aminci da hulda da ita. Sai a sawa manhajar ka’idoji. Yawancin kasashen da ake cewa a yanzu sun karbi tsarin, sun karba ne a dunkule, amma ba su sa dokikin da zasu maida Manhajar ta zamo karkashin Babban Bankin wadannan kasashe ba. Don haka kada wani ya rudu da zancen ai Akwai kasashen da suka yarda da tsarin.
ii- A dauki Bitcon a matsayin ‘kadara/haja’. Wannan kuma sai an sami kamfanonin da zasu rika juya Bicoin din a matsayin “share”, ta yadda kowace ‘share’ zata zamo a na ganinta cikin jumlar tsarin wadannan kamfanonin. A halin yanzu Bitcoin ba shi da wannan tsarin ta kowace fuska.
iii- Ya zamo kamar tsarin su ɓisa Card, Credit Card, da sauransu. Ta yadda za a sami wasu kamfanoni da zasu dauki gabaran gudanar da tsare-tsarensa da hadahadarsa da shige-da-fitarsa kamar yadda ake yiwa wadancan katika.
Yin ɗaya daga cikin wannan zai bawa Bitcoin wata sabuwar kima ta halacci a idon Musulmi.
A ƙarshe, hadahadar Cryptocurrency a karan kanta ba za a iya cewa haram ba ce, ba laifi Musulmin duniya su fara tunanin yadda zasu ci moriyar hakan ta hanyar da ta halatta wadda aka nuna a nan sama kadan. Saboda da alamu nan gaba kadan duk duniya za a raja’a a kan Degital Money. Amma dai a halin yanzu idan aka yi la’akari za a ga cewa wannan mu’amalla ta Bitcoin ta fada bangarori da yawa na haramci a Shari’ah, ba wai wani bangare daya ne kurum ba.
A ƙarshe muna yiwa Allah godiya, da fatan ya sa mun dace.
Farfesa Ahmad Mansur shine tsohon Shugaban Sashen Addinin Musulunci na Jami’ar Bayero
