Kotu ta haramta wa tsohuwar minista riƙe muƙami

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Wata babbar kotu a Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar Litinin, ta yanke hukuncin haramta wa tsohuwar ministar harkokin mata, Dame Tallen riƙe duk wani muƙamin gwamnati a cikin ƙara mai lamba CV/816/2016.

Don haka, Kotun ta bayyana cewa furucin Tallen ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki, rashin ɗa’a ne, rashin kunya, kiraye-kirayen ƙin bin hukuncin kotun, don haka ta raina babbar kotun tarayya ta Nijeriya.

Kotun ta kuma bayar da umarnin da ke hana tsohuwar ministar riƙe duk wani muƙami a Nijeriya, sai dai idan ta wanke kanta daga halin da ake ciki ta hanyar buga takardar neman gafara da kanta ga ’yan Nijeriya da ɓangaren shari’a a cikakken shafi na jaridun ƙasar.

Kotun ta bayar da umarnin cewa ta haramta wa wacce ake ƙara daga riqe kowane muƙamin gwamnati a Nijeriya har abada idan ta qi bin umarnin buga takardar neman gafara cikin kwanaki 30.

A ranar 14 ga Disamba, 2022, Hukumar NBA Incorporated Trustees ta gabatar da sammaci na asali a kan Tallen, wacce a lokacin ita ce ministar harkokin mata da cigaban jama’a, kan kalaman da ta yi a bainar jama’a game da hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke a kara mai lamba No. FHC/YL/12/2022 tsakanin Mallam Nuhu Ribadu da Jam’iyyar APC da wasu mutum biyu wanda aka gabatar a ranar 14 ga Oktoba, 2022.

Tallen a ranar 15 ga Oktoba, 2022 ta bayyana hukuncin kotun a matsayin “hukuncin rashin kam gado da ya kamata ‘yan Nijeriya masu kishi su yi watsi da shi.”

A wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan Nuwamba 14, 2022, Shugaban NBA, Yakubu Maikyau, ya rubuta wa ministar, inda ya buƙaci ta janye kalaman natanci da kuma miƙa neman gafara ga jama’a da kotun.