Tsofaffin ɗaliban makarantun kimiyya na Kano sun yi aniyar samar da jami’a

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kungiyar tsofaffin dalibai na makarantun kimiyya na jihar Kano sun ci alwashin samar da jami’a ta kungiyar.

Sabon Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Balarabe Jallah ne ya bayyana haka a jawabinsa na karbar jan ragamar kungiyar bayan rantsar da su a taron shekara da kungiyar ta gudanar a Jami’ar Bayero.

Ya ce duba da yawan da suke da shi na ‘yan kungiyar ya kamata a ce sun jawo hankalin masu ruwa da tsaki domin yara da suke fitowa daga makarantun kimiyyar da su rika fita waje suna karatu idan jami’ar ta samu za ta taimaka wajen fadada ilimi.

Ya ce yanzu haka a kungiyar suna da shugabannin jami’oi sun kai guda biyar banda tarin Farfesoshi da daktoci na kowane irin darasi yanzu sun kai shekarun da ya kamata a ce ‘yan kungiyar sun yi yunkuri sun kafa jami’a kuma da yardar Allah abu ne mai dorewa za su fara ne a hankali mataki-mataki har ya tabbata.

Balarabe Nuhu Jallah ya ce babbar gudummuwa da ‘yan kungiyar za su bashi shi ne na hadin kai in suka hada kai za su samu duk wani cigaba domin babu inda ba za ka samu yan kungiyar ba a ma’akatun gwamnatin tarayya da na jihohi da ‘yan siyasa da likitoci da lauyoyi da ‘yan kasuwa ba inda ba su shiga ba.

Ya ce manufarsu a kungiyar shi ne na gina dan adam ko da bayansu yara da suke tasowa za su cigaba da rike kungiyar in ka jawo su ka kyautata suma za su rama abinda aka yi musu a gaba.

Alhaji Balarabe Nuhu Jallah Dambatta ya nuna gamsuwa da jajircewa da ‘yan baya suka yi wajen kafa kungiyar da yanzu su ma suka zo suna shugabanci don haka a cigaba da ba su hadin kai da goyon baya don ci gabanta.