Duk wanda ya zama abin sha’awa a duniya mace ce ta mayar da shi hakan – Mariya Durumin Iya

“Rayuwar maraici da mutuwar aurena ne suka buɗe tunanina kan kafa gidauniya”

Daga AISHA ASAS

Rayuwar aure rai ne da ita tamkar dai yadda aka san dan adam da ruhinsa, yayin da mai shar’antawa Ya yi kira, ruhinsa ba zai kara ko sa’a daya a jikin ba, zai fice yana mai amsa kiran mahallici. Idan kuwa ba shi ya yi kiran nasa ba, ko duniya za ta taru don ganin ta tsayar da numfashinsa ba za ta iya tsayar da shi ba.

Haka ita ma rabuwar aure, daga auren har ranar karewar sa rubatacce ne, idan ranar rabuwa ta zo, ko da tsananin soyayya sai kaga an rabu, haka idan bai hukunta za a rabu ba, duk rikicin aure sai ki ga ya yi karko.

Duk da wannan sani da muke da shi, a Kasar Hausa, ana yi wa matan da auren su ya mutu mummunan fahimta, yayin da wasu ke shiga garari sakamakon zawarci.

Shafin Gimbiya na wannan mako ya samu bakuncin jajirtacciyar mace, da ke fafutukar wayar da kan al’umma tare da nusar da su muhimmancin tallafa wa matan da aurensu ya mutu, da wadanda mazajensu suka mutu, ga kuma uwa uba tarbiyya da ta ke koyarwa ga iyaye mata.

Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Mariya Inuwa Durumin Iya:

MANHAJA: Sunanki sananne ne, don haka tarihin rayuwarki ne muradin masu karatunmu.

MARIYA DURUMIN IYA: Assalamu alaikum. To kamar yadda yake makale jikin sunana, an haife ni a Unguwar Durumi Lokon Iya Marafa, kuma na yi karatu na addini da na zamani. Na yi karatun Al’kur’ani a nan unguwar ta Durumin Iya, makarantar allo, kuma a nan ne na yi saukar Al’kur’ani, Ina da shekaru 14, a makarantar Malam Danjummai.

Bayan kammala saukar na dora da karatun littafai, daga nan har zuwa makarantar dare da nake zuwa. Alhamdu lillah, karatun addini an same shi daidai gwargwado, saboda ko karatun nawa na bokon ma na yi shi ne a vangaren addini.

Na yi makarantar firamare a Guma Primary School, sannan na karasa a Gidan Galadima. Sai kuma makarantar gaba da firamare da na yi ta a ‘Kuliyyattul Tarazzul Islam’ Gwarzon Dutse. Makaranta ce da marigayi Sheikh Nasir Kabara ya yi. To alhamdu lillah, na san daga cikin sunan ma za a fahimci ta ilimin addini ce.

Bayan nan kuma na yi karatu a bangaren shari’ar Musulunci, wato Islamic Law, a Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies. Sannan na yi karatun ‘Education’ a ‘Islamic Studies a matsayin digiri na na farko, a Jami’ar Maitama Sule. Sai kuma digiri na biyu wanda nake kai yanzu a Jami’ar Bayero, shi ma dai akan ‘Education’ din ne, amma a bangaren ‘Adult and Non-formal Education’. Wannan shi ne abinda ya shafi bangaren karatu kenan.

A bangaren rayuwa, alhamdu lillah, Ina da aure, kuma Ina zaune da maigidana lafiya. Sannan mahaifina ya rasu tun ban fi shekaru 16 ba. Ina tare da mahaifiyata da ‘yan’uwana. Alhamdu lillah. Ina ‘yan kananan kasuwanci namu na mata, sannan Ina gudanar da aikin gidauniya ta.

Kin kasance daya daga cikin jajirtattun matan Arewa da ke fafutukar nema wa ‘yan’uwansu sasauci kan radadin talauci, ta hanyar samar masu da ababen bukatu. Za mu so jin yadda wannan tunanin naki ya samo asali.

To alhamdu lillah. Wato ni har kullum Ina kallon kowacce matsala ta mata, na kan yi kokarin ganin na zurfafa tunani kan wai mai ya janyo matsalar ne? Menene asalin abinda ya janyo fatuwar matsalar koma wacce iri ce. Ba ma ta mata ba kawai, domin duk matsalar da aka ga ta faru, to kamata ya yi a maida hankali akan gano ainahin menene matsalar, me ya jawo ta.

To, ni nawa tunanin akan ‘yan’uwana mata ya samo asali ne kamar yadda na fada a baya ni marauniya ce. Na fara rayuwar maraici tun shekara daya bayan kammala karatun sakandire. Kuma ni ce karama a gidan. To gaskiya ga wanda ya san yadda rayuwa da mahaifa ta ke, yadda maraici yake, ya san idan aka ce mutum ya rasa mahaifinsa tun ma a ce bai ma wani girma sosai ba, gibi ne mai girma.

Bayan nan kuma sai na zo na yi aure, sai muka rabu da maigidana, to wannan rabuwar auren nawa ta sa tunanina ya dada budewa kan ababen da suka shafi rayuwar mata a lokacin da ta rasa iyayenta da kuma yadda take rayuwa a lokacin da ba ta da miji. Yadda mace take rayuwa a irin wannan lokaci kusan za a ce ba ta da gata. Duk da cewa, a bangare na ni bazan ce na yi rayuwa ta rashin gata ba, don ban bari zuciyata ta mutu ba, asalima ban tava yarda na amince cewa, ba ni da gata ba, domin idan har ka amince ubagijin ka na nan, kana da ranka da lafiyarka, to ba za ka kira kanka marar gata ba.

To, tun daga wannan lokacin da hakan ta kasance gare ni, sai nake tausayin mata, tare da yi masu uzuri kan wasu ababe, sannan na kan fahimci inda matsalar su ta samo asali yayin da suka bayyana min ita. Shin irin tawa ce, wato auren ta ne ya mutu, ko mijinta ne ya mutu, kuma dangin nasa ba su karvi dawainiyar ta ko ta ‘ya’yanta ba, koko da auren ta ya mutu ta dawo gida, iyayenta ba su karvi dawainiyar ta, tana da sana’a, tana aiki ne, yaya ta ke gudanar da rayuwarta? Ire-iren wadannan tunanin ne ya sa na hango budatar wayar da kai ga matan. A dinga tunantar da mu rayuwa, kar mace ta dauka cewa, idan auren ta ya mutu, ko mijinta ya mutu, ko idan ba ta samu miji ba, ko ba ta yi aure da wuri ba, kamar shi kenan rayuwarta ta zo karshe.

A’a. Akwai gudunmawa da yawa da za ta iya ba wa kanta da kuma al’umma koda ba ta da aure. Shi aure kaddara ce da Allah ne mai hukunta wanzuwar sa ko akasin hakan, kuma rashin samuwar sa a kanki ba yana nufin kin yi wa Allah laifi ko ba Ya son ki ba, domin akwai bayin Allah mata da dama da muka ji tarihinsu da wasu darajarsu mai yawa ce da annabta ne kawai ba a ba su ba, amma sun yi rayuwarsu ba tare da an kaddara masu aure ba.

To kinga idan muna kallon irin wadannan za mu ga lallai akwai gudunmawar da mata za su iya bayarwa a cikin al’umma wadda ba lallai sai tana gidan miji ba, ko sai ta rayu rayuwar jin dadi, irin a ce, tana da miji, tana da uba ba, a’a. Kowacce mace akwai irin baiwar da Allah Ya yi mata, wadda idan ta tsayu akan ta, ta jajirce, za ta more kanta, wasu din ma za su more ta.

To wannan ne dalilin da ya sa na ce, kar na kashe zuciyata, bari na yi, wataqila daga ni, wasu matan ma za su kwaikwaya, su jajirce akan kansu don su inganta rayuwarsu.

A matsayinki ta mai jan ragamar Gidauniyar Wayar da Kai da Cigaban Al’umma, (Foundation for Social Orientation and Gender Development). Za mu so sanin yadda wannan gidauniyar ta soma.

To alhamdu lillah. Gidauniyar Wayar da Kai da Cigaban Al’umma, wato ‘Foundation for Social Orientation and Gender Development’, ta kafu shekaru uku da suka wuce, ranar 18 ga watan Disamba, shekara ta 2020. Ita ce ranar da na karvi satifiket din ta daga CAC, don haka nake daukar wannan rana a matsayin ranar da gidauniyar ta kafu. Kuma alhamdu lillah, wannan gidauniyar ta samo asali ne daga wancan tunanin nawa, na yaya zan taimaki mata ‘yan’uwana, wadanda suka samu kansu a irin rayuwar da na samu kaina a ciki.

Yawanci za ki ga idan aka ce mace aurenta ya mutu, ko mijinta ya mutu, kallon farko da mutane ke yi mata shi ne, wannan macen zaman kanta ta ke yi, musamman wadda ta ke fita ta nemi halalin ta, ta ke fafutar neman na rufa wa kai asiri, ta ke ‘yan kasuwancinta haka, saye dai da siyarwa, ko kuma tana aiki, sai a dauka wannan macen zaman kanta ta ke yi, ta fi karfin kowa, ba ta son zaman aure, ba ta da hakuri, ta zabi wata rayuwa marar kyau.

To kuma idan ta zo ta zauna din, ba ta da auren, kuma ba ta komai, ba fa wanda zai dau nauyin nata, ba wanda zai dauke mata bukatunta, tunda dai shi mijin ya riga ya sake ta. Hakan na nufin idan ta zauna din ciwon damuwa ne zai kamata ko Ire-iren curutan nan da kuncin rayuwa zai iya janyowa.

To a lokacin da na gama digiri dina na farko, muna zaman jiran sakamakon, sai ya zama an fada yajin aiki. Wannan tafiya yajin aikin da aka yi, ya taba ni kwarai da gaske, domin zakuwa da muke yi na ganin sakamakon, don ka ga ka ci ko ba ka ci ba. Yajin aikin dai ya dauki tsayin watanni 8, don haka a wannan lokacin ne na yi tunanin Ina ta zaune a gida, tunda ba na aiki, Ina tambayar kaina me zan yi?

To sai na yi duba da rayuwar da na yi a jami’a, na fahimci abubuwa da yawa na lalacewar tarbiyya, wanda a lokacinmu ba haka suke ba, domin a lokacin da na yi difloma ne na yi aure, sai kuma muka rabu da mijina, sannan na sake komawa karatun, wato digiri dina na farkon. To a wannan lokacin da na kalli yadda rayuwar mata ta zama a jami’a da abubuwan da ake yi a ciki, sai na ke mamaki, yaushe al’ummarmu ta zama haka ne? Yaushe lalacewar tarbiyyarmu ta zama haka?

To bayan mun gama karatun, mun tafi wannan yajin aikin, sai na fara tunanin yadda zan iya bayar da tawa gudunmawar. To a nan ne tunanin yin rubutu kan tarbiyyar mata ta zo min, wataqila koda ni ban mora ba, tunda ba ni da ‘ya ko dan da zan yi wa tarbiyya yadda ni ma aka yi min, idan na bari a rubuce, wata rana wasu za su duba, kuma zai amfane su a tarbiyyar nasu ‘ya’yan. Kinga kuwa zan samu wannan lada.

Da wannan na fara rubutu, wanda har ya kai ni ga rubuta littattafai guda uku; daya akan almajiranci ne mai suna ‘Almajiranci da Bara’, sai kuma wanda na yi akan tarbiyya mai suna ‘Rayuwar Mace daga Haihuwa zuwa Tsufa’, sai kuma ‘Soyayya da Rayuwar Aure a Kasar Hausa’ wanda shi ma ya shafi tarbiyya, amma akan abinda ya shafi zamantakewar aure.

To bayan na kammala wadannan littattafan, aka yi bikin kaddamar da su, sai kuma tunanin kafa wannan gidauniyar ya zo min. A lokacin akwai wani wanda baba ne a wurina, ya ce, tunda wannan damar ta samu, domin a lokacin alhamdu lillah an fara gayyata ta gidajen rediyo da na talbijin, yin shirye-shiryen da suka shafi tarbiyya, da wanda ya shafi wayar da kai, zamanantar aure, to shi ne fa ya ce, me zai hana mu yi abinda zai ba wa mutane dama su iso gare mu da matsalolinsu, ta yadda za a iya samun mu kai tsaye, a yi magana da mu, a tattauna, watakila hakan zai sa a samu mafita.

To da wannan shawarar na duba, a matsayina ta dalibar shari’a, duk abinda zan yi na fi son in yi shi bisa tsari da kuma ka’ida, don haka sai na ce bari na yi abinda zai kasance na samarwa kaina aikin yi kuma har na samar wa wasu. To da wannan ne wannan tafiya ta fara, wadda nake fatan ko bayan raina, ko kuma idan aka wayi gari ni na dena, wasu su tallafe ta, su ci gaba da yi. Saboda ba mai burin ya asassa wani alheri a ce ya tsaya.

Zuwa yanzu kuma ba abinda za mu ce sai alhamdu lillah, domin cikin ababen da muke yi akwai taruka na wayar da kai akan wasu matsaloli, musamman ma abinda ya shafi tarbiyya da zamantakewar iyali. Tunda shi ne babban jigon mace, a bata tarbiyya, ita ma ta bayar, ta kula da iyali. Duk wani da aka gan shi abin sha’awa a duniya to mace ce ta mayar da shi hakan. Akasin haka ma za mu iya cewa daga macen ne.

Fatanmu rayuwar mata ta inganta, su zama abin sha’awa, a daina yi wa mace marar aure mumunan fahimta, a ba su dama su ma a ga nasu kamun kan, wanda watakila wata ta fi ma mai auren kamun kai.

Menene ayyukan wannan gidauniyar?

A nan za mu dasa alamar tsayawa a wannan tattaunawa da muke yi da Mariya Inuwa Durumin Iya, inda da yardar mai dukka, a sati mai zuwa za mu fara da samar wa masu karatu amsar tambayar da muka tsaya kanta, kafin mu tsunduma tattaunawa kan sha’anin aure da saki tare da tarbiyyar ‘ya’ya mata, da sauran ababen da bakuwar tamu ta yi fice kansu.