Gobe majalisun tarayya za su yi zaman ƙarshe kan Kasafin 2024

Daga BASHIR ISAH

Gobe Juma’a ake sa ran sanatoci da ‘yan majalisar wakilai za su yi zama domin amincewa da kasafin 2024 wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar musu.

Sanata Opeyemi Bamidele, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin a Jihar Ekiti.

Sanatan ya ce dukkan ‘yan majalisun tarayya za su katse hutunsu domin yin wannan inda za a amince da kasafin 2024.

“Don tabbatar da an amince da kasafin a kan lokaci, ya sa muka bukaci baki daya ma’aikatu da hukumomi su bayyana gaban hadakar kwamitocin Majalisar Dattawa da ta walakilai.

“Wanda hakan ya taimaka wajen rage lokacin da akan dauka wajen kare kasafi, sabanin yadda a da sai an fara bayyana gaban Majalisar Datawa, sannan daga bisani a je ga Majalisar Wakilai,” in ji Sanata Bamidele.

Ya kara da cewa, sun yi zama fiye da yadda suka saba, har a ranakun Asabar sun yi zama duk dai da zummar ganin kasafin 2024 ya cimma nasara.

“Za mu yi zama a ranar 29 ga Disamba. Fatanmu shi ne amincewa da Kasafin ya zuwa ranar 30 ga Disamba. Ta yadda a ranar 1 ga Janairun 2024, Kasafin ya isa gaban Shugaban Kasa a matsayin doka don ya rattaba hannu,” in ji shi.