Rasuwar Ghali Na’abba babban rashi ne ga ƙasar nan – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Fitaccen dan kasuwa basarake Dan-Saran Kano, Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya bayyana mutukar alhininsa bisa rasuwar tsohon kakakin majalisar wakilalai na Nijeriya, Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba.

Ya bayyana cewa rasuwar Ghali babban rashi ne ba ga jihar Kano kadai ba har ma da Arewa da kasa baki daya. Sannan fitaccen dan siyasa ne wanda ya yi gwagwarmaya domin tabbatar da adalci a tsarin tafiyar da dimukradiyyar kasar nan.

Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya ce a lokacin da yake kakakin majalisar wakilai kowa ya shaida a kasar nan, bai zama dan kanzagi ko dan amshin shata ba, ya yi ta kokari domin kare muradun al’umma, hakan ta sa wasu ke ganin ya zame wa gwamnatin wancan lokacin kadangaren bakin tulu.

Ya kara da cewa irin wannan jajircewa da tsayuwar daka akan gaskiya ake so ‘yan majalisun mu da sanatoci musamman na Arewa su tsaya akai domin ceto al’umma daga halin kunci na son rai da aka jefa al’ummar kasar nan suke dada shiga halin matsin rayuwa.

Ya yi fatan Allah ya bai wa al’ummar Kano da Arewa juriya na wannan babban rashi da aka yi na tsayayyen dan siyasa mai son ci gaban al’umma.

Dan-Saran na Kano ya kuma miqa ta’aziyya ga ‘yan kasuwar jihar Kano musamman na kasuwar Kantin Kwari bisa rasuwar daya daga shugabanni da suka rike kasuwar, Alhaji Sharu Sagir.

Ya ce Sharu Sagir mutum ne mai amana mai da karvar shawara da girmama mutane da ya bada gagarumar gudummuwa wajen hada kai da ci gaban ‘yan kasuwar Kantin Kwari.

Alhaji Gambo Muhammad Danpass ya kuma yaba wa gwamnatin  jihar Kano da cewa ta ciri tuta wajen gudanar da ayyuka daban-daban don cigaban al’umma karkashin zababben Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Dan-Saran na Kano ya yi fatan al’ummar jihar Kano za su ci gaba da bashi hadin kai da goyon baya da addu’o’i domin samun nasarar cigaba da aiwatar da ayyukan alkhairi domin ci gaban jihar.