Ɗan majalisa ya tallafa wa makarantar Islamiyya a Funtuwa

Daga DAUDA USMAN a Legas

Dan malalisar dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Karamar Hukumar Funtuwa a zauren majalisar jihar Katsina Hon, Abubakar Muhammed Total Funtuwa kuma Shugaban Kwamitin Lafiya a majalisar jihar Katsina ya bai wa wata makarantar Islamiyya a mazabarsa mai suna Anwaruddin Islamic Centre Funtuwa gudunmawar kudi har Naira dubu dari biyar a matsayin gudunmawar da makarantar take nema a hannuwan al’ummar Musulmi domin ara fadada ajijuwan makarantar baki daya.

Dan majalisar dokokin na jihar Katsina Hon, Abubakar Muhammed Total Funtuwa ya bai wa makarantar wannan gudummawar ce a Funtuwa a lokacin da makarantar ta Anwaruddin Islamic Centre Funtuwa take gudanar da taron walimar yaye dalibanta maza da mata guda hamsin karo na goma sha shida a harabar makarantar dake kan layin Takakare Zamfarawa cikin garin Funtuwa a ranar Asabar din makon jiya.

Gudunmawar kudin wanda Daraktan makarantar Malam Samaila Ibrahim dan Malam da sauran ‘yan kwamitin makarantar suke neman taimako a hannuwan al’ummar Musulmi domin biyan kudin wani gida da ya yi iyaka da makarantar wanda za su biya kuma su rushe shi domin su samu filin kara fadada azuzuwan bangarori da sauran wuraren biyan bukatun daliban makarantar gaba daya.

Bayan kammala jawaban taron walimar yaye daliban makarantar ne makarantar ta Anwaruddin Islamic ta karrama shugaban kungiyar Izala na Nijeriya Sheikh Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe tare da ba su lambar yabo a kokarinsu na daukaka addinin Musulunci a yayin da aka ummarci wakilin Gwamnan jihar Katsina a wurin taron Hon, Abubakar Muhammed Total Funtuwa ya mika musu lambar yabon a hannuwan su guda biyu sannan dan majalisar ya cigaba da bai wa shuwagabannin makarantar hakuri da su yi hakuri da a bin da suka samu na gudummawar a hannunsa sakamakon rashin gaya masa da ba a yi da wuri ba.

Haka zalika Abubakar Muhammed Total ya cigaba da isar da sakon godiyarsa ga al’ummar mazavarsa ta Funtuwa da kewayenta gaba daya a cewarsa bisa ga jajircewar su tare da hadin kai da goyan bayan da suke ba shi a kowane lokaci idan hakan ta taso.

Bugu da kari ya ce kuma a matsayinsa na wakilinsu a majalisar Jihar Katsina zai cigaba da kawo ci gaban karamar hukumar Funtuwa a kowanne lokaci kamar yadda ya saba yi yau da kullum.

Karshe ya ce yana mai shawartar al’ummar jihar Katsina da kewayenta da su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar Katsina hadin kai da goyan baya a kokarin ta na kawo tsaro dama ci gaba jihar ta Katsina baki daya.