Ƙungiyar ‘yan jarida ta karrama Shekh Rigi-rigi Kusfa

Daga ISA GIDAN BAKKO a Zaria

A makon jiya ne Kungiyar Mawallafa Jaridu ta Arewa ‘AREWA PUBLISHEUM’ ta karrama fitaccen malamin addinin Musuluncin da ke Zariya mai suna Malam Usman Bini Shekh Idris Kusfa, saboda jajircewarsa wajen ilmantar da al’umma ilimin addinin Musulunci a ciki da kuma wasu kasashe da ke makotaka da Nijeriya.

Taron karrama fitaccen malamin ya gudana ne a Zawiyyarsa da ke Unguwar Kusfa a Birnin da kuma ya sami halartar muridansa da kuma wasu fitattun malamai da suke Zariya.

Dokta Sani Garba shi ne mataimakin shugaban kungiyar da ya jagoranci karrama wannan malami, ya ce kungiyarsu ta karrama wannan malami ne a bisa binckennda suka yi na fahimtar yadda ya tashi tsaye wajen ganin al’umma sun sami ilimin addinin Musulunci da zai masu jagora na rayuwarsu ta yau da ta gobe.

Dokta Garba ya yi amfani da wannan dama,inda ya yi kira ga malaman addini a duk inda suke a tarayyar Nijeriya da suran kasashen da suke sassan duniya da su riqa koyi da Shekh Usman Rigi-rigi na yadda ya ke koyarwa ba tare da suka wani malami ko kuma suka wata fahimta ba, wannan a cewarsa, shi ya haifar ma sa da samun daukaka a Nijeriya da kuma wasu kasashe da suke makwabtakata da Nijeriya.

Da kuma ya juya ga muridansa Shehin Malamin, Dokta Sani Garba, sai ya yi kira gare su da su ci gaba da amfani da koyarwa da ya ke yi ma su a duk inda suka tsinci kansu a nan gaba.

A jawabinsa bayan ya karvi karramawar Shekh Usman Rigi-Rigi Kusfa ya nuna matukar jin dadinsa na wannan karramawar da aka yi ma sa,inda ya ce, ya sami karrama da dama a rayuwarsa, amma wannan karramawar da wannan kungiyar ta yi masa a cewarsa, ta sha gaban sauran karramawar da ya samu a baya.

Kuma ya kara da cewa, tabbas ya kara samun kwarin gwiwar kara tashi tsaye na ganin ya sauke nauyin da Allah ya doar al’ummar da al’umma ilimin addinin Musulunci da kuma kara inganta rayuwarsu da za su zama al’umma da za su yi amfani a kasarsu baki daya.

Shekh Usman ya kuma yi amfani da wannan dama na yin kira ga Gwamnatin Tarayya da kuma na jihohi da su kara tashi tsaye, na ganin sun inganta kayayyakin aiki a gidajen rediyo da suke jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya, domin a sami kafar da za ta ilmantar da al’umma ilimin addinin Musulunci da kuma samar da shugabanni nagari daga sauraron kafafen watsa labaran.

Shehin Malamin ya yi amannar cewar, matukar al’umma suka sami ilimin addininsu, za a sami lafiya a kasa,da zai kawo karshen duk wata matsala da ke addabar al’umma, da ta shafi rikicin da ake alakanta shi da addini da rashin tsaro da kuma inganta zamnkewar al’umma.

Shekh Usma Bini Shekh Idris Kusfa ya kammala da kira ga manema labarai da suke aiki a kafafen labarai a tarayyar Nijeriya da su kara tashi tsaye wajen bin dokokin aikin jarida, ta yadda za su nisanta kansu daga rubuta wa ko bayyana wasu labarai da za su kawo matsaloli a kasa ko a tsakanin mabiya addini da suke Nijeriya.