2024: Gwamna Raɗɗa ya rattaɓa hannu kan kasafin N454.3bn

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dikko Umaru Radda ba Jihar Katsina ya rattaba hannu kan kasafin 2024 ya zama doka biyo bayan amincewa da kasafin da Majalisar Dokokin Jihar ta yi.

A ranar Laraba Gwamnan ya sanya wa kasafin hannu a Fadar Gwamnatin Jihar, kasafin da jimillarsa ta kai N454,308,862,113.96.

Da yake jawabi bayan rattaba hannu kan kasafin, Gwamna Radda ya yi gidiya ga majalisar jihar bisa hanzarin da suka yi wajen dubawa da kuma amincewa da kasafin a cikin kwana 33.

Kazalika, ya jinjina wa Mataimakin Gwamnan Jihar da majalisar zartawa da daukacin wadanda suka bada gudummuwa wajen kammaluwar kasafin.

Daga nan, Radda ya bada tabbacin bin kasafin daki-daki kuma daidai da tsarin doka wajen aiwatar da kunshiyarsa don amfanin jihar da al’ummarta.