Ilimin manya makami ne na gyara al’umma – Amina Ahmed Gumel

“Rashin Turanci ne ke taka wa mutanen mu birki a Turai”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR

Amina Ahmed Sani Gumel ‘yar Nijeriya ce wanda ta ke zaune a Kasar England inda ta ke koyar da ilimin manya masu koyon yaren Turanci a matsayin yare na biyu.

A cikin tattaunawarta da wakilin manhaja, ta kawo irin hanyoyin da suke bi wajen koyar da mutane baqi yaren Turanci wanda zama ya kama su a Kasar England. Haka kuma ta kawo irin qalubalen da ta fuskanta wajen yaren Turanci dama irin nasarorin da ta samu a matsayin mai koyar da yaren Turanci a Kasar England. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Za mu so ki gabatar mana da kanki ga masu karatun mu.

HAJIYA AMINA: Assalamu alaikum. Ni dai sunana Amina Ahmed Sani Gumel, an haifeni a garin Gumel da ke Jihar Jigawa. Na taso a garin Gumel inda na yi makarantar firamare bayan kammalawa mun koma Kano inda na yi makarantar sakandare ta WAT da ke Gwauron Dutse. Bayan kammala sakandare na sake dawowa Gumel inda na shiga makarantar koyar da malamai ta ATC inda na karanci ‘Business Education’.

Bayan kammala NCE na samu aikin koyarwa a wata firamare anan garin namu na Gumel. Bayan da maigidana ya samu damar tafiya karin karatu a nan England sai ya zama muka taho tare inda na ci gaba da karatu har na samu shaidar karatu daban-daban kamar HNd Business Studies And Accounting sai kuma na yi BA shima akan Accounting.

To da yake Turai ba kamar qasarmu ba ce, bazan iya aiki a banki ba tunda ina da yara sai ya zama na koma vangaren koyarwa tunda dama tun a Nijeriya na samu shaidar koyarwa. inda na yi PGEC akan koyar da turanci ga wadanda suke baki.

Bayan na kammala na samu damar koyarwa a kwalejin ilimi da jami’o’i inda na sake komawa na yi digiri na biyu akan koyar da turanci ga baki.

Yanzu haka na samu ‘Certificate’ akan koyar da mutane masu shigowa domin karin karatu yi masu jarrabawa. Haka kuma Ina cikin masu nema wa baki masu shigowa karin karatu da kula da su tare da taimaka musu.

Menene ake kira da shi kansa ilimin manya?

To idan aka ce ilimin manya yana nufin ilimi ne mai dogon zango wanda ya kunshi mutane da suka fara daga shekaru 18 zuwa sama, wanda kuma ya zama zai dauki tsawon lokaci kafin a gama. Karatun da idan yaro ne zai gama shi a kankanin lokaci, amma saboda rashin cikakken lokaci zai zama dole sai a hankali ake yin sa.

ilimin manya kusan mutumin ne da kansa zai jagoranci kansa wajen karatun, Ina nufin shi ne zai tsara lokacin da yake ga zai iya yi dama yin sa a lokacin da ya ga yana da dama. Ilimin manya a kimiya mun dauke shi a matsayin makami wanda zai taimaka wajen samar da al’umma ta gari wajen ba wa al’umma dama su tsara rayuwar gabadaya. Wannan zai saka su samu damar gudanar da komai nasu ba tare da wani ya shiga wajen tallafa masu ba.

Misali ka dauka anan Turai, za ka ga mutanenmu suna shan wahala wajen rayuwa sakamakon rashin ilimin turanci, dole idan mutum zai je cefane, asibiti, kasuwa dole sai da turanci. Wannan tasa dole sai dai ka ga mutanen mu suna daukan wanda zai musu tafinta daga yarensu zuwa turanci, kaga wannan zai zama baka da sirri kamar ka je gun likita dole wani ne zai fada masa ga abinda ke damun ka, ko da kana fama da wani abu wanda yake bukata sirri.

Da yake kina koyar da Turanci ga bakake. Ya ki ke ganin tasirin da yaren yake da shi ga masu shiga kasashen ketare?

To a gaskiya wannan ba karamar matsala ba ce, yawanci rashin turanci yakan taka wa mutanen mu birki wanda suka samu kansu a Turai , za ka ga rashin turanci ya jawo ma mutum wata matsala da zai dauki tsawon shekaru kafin ya warware ta.

Za ka ga wani lokacin mutanen mu suna fama da rashin gane karatu dama na ce maka ilimin manya yakan dauki tsawon lokaci kafin a gama shi, wannan kansa wani lokacin mutanen mu kan sha wahala wajen koyan turanci.

Dama kuma duk wanda ya karanci koyarwa ya san akwai bambanci halitta da Allah ya yi ma kowa. Za ka ga wasu sun fi so ka nuna musu da hannu yadda za su gane, wasu dole sai ka nuna musu hoto sannan zasu gane, wasu dole sai ka rubuta musu sannan za su gane. Shi ne ya sa za ka ga babu style takamaiman da ake koyarwa da shi, kowane malami yana amfani da hanyar da yake ganin yawancin dalibain sa suke ganewa. Wasu sun fi so ka ba su da hannunsu su gwada.

To kaga koyar da shi yana da tasiri sosai wajen rayuwa a kasashe kamar Turai. za ka ga koda su Turawa idan kana koyar dasu zaka kusan iri daya ne da namu bakaken bai wuce bambanci dake akwai ba na su dama yarensu ne na mahaifiya wannan kusan shine yake bambanta mu da su.

Haka kuma anan za ka ga su suna da tsarin cewa duk wanda ya shigo dole ne ya koma ya yi karatu ba za su baka gida suna ciyar da kai ba ka komai, dole ne sai ka je ka koya don haka gwamnatin zata biya kudi musamman ta dauki mutane wadanda za su koyar da su ilimin turanci. Saboda su suna da tsarin na duk wanda yake aiki akwai wani haraji da yake bama gwamnatin wanda da shine ta ke daukan nauyin al’ummarsu marasa karfi.

Don haka dole gwamnatin qasar ta saka ya zame maka dole sai ka je ka koyi yaransu wajen ciyar da kasarsu gaba. Kaga wannan ya sava da irin kasashen mu ba a kula da ilimin mutane ballantana ya zama wani abu da za a daukan nauyi karatunsa har ma ya zama yana aiki ana samun haraji daga gun sa.

So da a ce qasashe kamar Nijeriya za ta dauki irin wannan tsarin na bama mutane manya wanda shekarun su suka wuce 18 su rinka shiga makarantun yaki da jahilci za ka ga an samu tafiyar karanci ilimin manya da muke fama da shi wanda hakan zai taimaka wajen kashe rashi aiki yi da zaman kashe wando a kasarmu.

Wadanne kalubale kibka fuskanta a kashin kanki a matsayin mai koyar da turanci a Kasar Ingila?

To a gaskiya babban qalubalen da na fuskanta anan shine, yanayin tarbiyyar yara kaga mu Musulmai ne bama wasa da tarbiyya irin ta Musulunci, wannan tasa na ki yin aikin banki kaga a banki baka da lokaci iyalanka tare da ba su ilimin addini wannan tasa dole na koma vangaren koyarwa inda duk lokacin da ake hutun dalibai ni ma Ina hutu, Ina kuma kula da karatun yaran namu.

Haka kuma kalubale na biyu shine, kaga ni na zo a matsayin mai ilimi wanda nasan turanci, amma tunda da maigidana muka zo sai ya zama a jikin Visa ta babu damar yin aiki wannan ya sakani cikin wani hali amma daga karshe wannan ya wuce.

Haka kuma wani kalubalen da na fuskan shi ne, mu acan za a baka kayan karatu ka je ka karanta ka yi jarrabawa ta kuma ci, amma anan sai fa ka yi da gaske za a koya muku komai ne yadda yake a baku komai na aiki ku rubuta aka dole sai kwakwalwa ka ta yi aiki wajen samar da wani abu, to kaga babu damar yin abu ba da gaske ba to gaskiya wannan tsarin ya wahalar dani amma daga karshe shima an wuce gun sa.

Wadanne nasarori ki ka samu?

To, alhamdu lillah, gaskiya an samu nasarori kamar damar koyarwa a jami’a da kwalejin ilimi ina koyar da turanci a matsayina ta bakar bata, to kaga wannan ba karamin abu ba ne. Haka kuma na samu damar ci gaba da karatu kusan kowane lokaci duk inda naga wani abu da akace koyar da ilimi ne za ka ga ina kan gaba wajen samun damar wannan ilimi. Haka kuma Ina karatun addini karka tsaya a guri daya ka nemi duniya ka kuma nemi lahira.

Wacce shawara ki ke da ita ga gwamnatin Nijeriya wajen inganta bangaren ilimin?

To a gaskiya Ina da kira musamman ga shuwagabannin mu wajen ganin an inganta bangaren ilimi domin samar da cigaba mai dorewa, haka kuma ina da buri ace gwamnatin kasarmu za ta yi amfani da dama da muke da ita wajen nemo mu mu zo mu bada gudunmawar mu a janibin ilimi wanda haka zai taimaka wajen karancin ilimi da muke fama da shi.

Mun gode.

Ni ma na gode.