Gwamna Lawal ga sabbin alkalai, ku zamo masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da ke kanku

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya kalubalanci sabbin alkalai (Khadis) na Kotun Daukaka Kara ta Shari’ar Musulunci a jihar da su zamo masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.

A ranar Laraba Babbabn Alkalin Jihar ya rantsar da sabbin Khadi a Fadar Gwamnantin jihar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta nuna kotunan shari’a na taka muhimmiyar rawa a tsarin shari’ar jihar.

Bala Idris ya bayyana cewa a 1999 ne aka fadada kotunan shari’a a Jihar Zamfara inda suka fara sauraren shari’a kan manyan laifuka da sauran batutuwa wanda tuni aka tasirin ayyukansu.

Sa’ilin da yake jawabi, Gwamna Dauda Lawal ya yi kira ga sabbin Khadin da su kiyaye martaba da mutunci ofishinsu.

Ya ce, “Na yi amannar cewa mukamin Khadi da aka nada ku a Kotun Daukaka Kara ta Shari’a na da nasaba da kwarewarku, fahimtar hukunce-hukuuncen Muslunci da kuma kwazon da kuke da shi wajen aiki da Shari’a.

“Kuna da rawar da za ku taka wajen tabbatar da adalci ga jama’a a wajen shari’a, don haka amanar da ke kanku babba ce. A matsayinku na khadi, ku rika tuna cewa Allah zai tambaye ku game da ayyukanku a Ranar Kiyama,” in ji shi.

Kazalika, Gwamna Lawal ya bukaci sabbin alkalan da su rike amanar jama’a a tsarin shari’ar Musulunci tare da tabbatar da kotu ta zama wurin da mara gata zai je don samun adalci.

A cewarsa, “Daidai da kudurin gwamnatina, za mu yi kokari wajen aiwatar da shari’a a sassan jihar baki daya.

“Bayan rantsar da ku da aka yi yau, ku saka a zukatanku cewa akwai babban aiki a gabanku na kare martabar tsarin shari’ar Musulunci. Dole a yi wa kowa adalci ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.”