Janar-janar 113 sun yi murabus daga Sojin Nijeriya

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Wata sanarwa daga rundunar Sojin Nijeriya ta yi nuni da cewa, janar-janar su 113 ne suka yi murabus ko kuma ke shirin yin murabus daga sojin Nijeriya a wannan shekara ta 2023.

Sanarwar da ta yi wannan bayanin ta fito ne ta bakin Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, a ranar Laraba, 20 ga Disamban 2023.

Sanarwar ta kara da cewa, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi yabo da jinjina ga manyan jami’an sojojin da lamarin ya shafa bisa sadaukarwar da suka yi wajen yi wa kasa hidima bil hakki.

Abubakar ya yi wannan yabo ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron dina da aka shirya wa jami’an Asokoro, Abuja.

Ministan ya bai wa jami’an tabbacin samun hakkokinsu na fansho ba tare da bata lokaci ba.

Jami’an da lamarin ya shafa sun hada da Janar 1, Laftanar Janar 1, Manjo Janar Major 67 da kuma Brigediya Janar 44.

By Editor