Da Ɗumi- ɗumi: ’Yan Majalisar Zamfara sun yi wa Kwamishinan Kasafi korar kare

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta kori Kwamishinan Kasafi da Tsarin Tattalin Arziki na Jihar, Hon. Abdulmalik Gajam, gabanin Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya gabatar da kasafin 2024.

Yayin zamansu a ranar Alhamis, ’yan Majalisar sun ce an kori Kwamishinan daga zauren ne saboda kin amsa gayyatarsu a can baya.

Kazalika, ’yan Majalisar sun yi barazanar janye hurumin da ya bai wa Gajam damar zama Kwamishinan jihar.

Daga bisani, Gwamna Dauda ya gabatar wa majalisar kasafin 2024 kamar yadda aka tsara tun farko.

By Editor