Yadda sunayen manoman bogi suka mamaye shirin bunƙasa noman alkama a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Gwamnatin Tarayya ta sha ɓullo da muhimman shirye-shirye da tsare-tsaren farfaɗo da harkokin noma, don inganta tattalin arziki, ayyukan yi tare da samar da isasshen abinci ga al’ummar ƙasa baki ɗaya. Wanda a zahiri, waɗannan muhimman shirye-shirye; idan an aiwatar da tsarin da yake a rubuce a takardun bayanai, hakan zai taimaka wajen kawo mafita ga wasu daga cikin wahalhalun da yan Nijeriya suke fuskanta na ƙarancin abinci da hauhawar farashinsa.

Shirye-shiryen tallafa wa ayyukan da za su farfaɗo da aikin noma tare da manoma sun haɗa da amfani da ƙungiyoyin manoma na ƙasa, waɗanda suka ƙunshi ‘North East Commodity Associations (NECAS)’, da na ‘Rice Farmars Association of Nigeria (RIFAN) da makamantan su. Yayin da wani zubin ma’aikatar kula da aikin noma ta ƙasa ce ke ɗaukar nauyin aiwatar da shirin, da zimmar ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, amma daga bisani haka al’amarin zai wuce kamar hurawar iska.

Gwamnatin Tarayya da na jihohin sun sha ƙurin bayar da tallafi don farfaɗo da harkokin noma daban-daban, kama daga noman alkama, shinkafa, rogo, masara, da makamantansu. Tsarin da ya qunshi bai wa manoma bashin da babu ruwa, kayan noma (motocin noma da sauran kayan noma na zamani), tallafin kaso mai yawa, domin sauƙaƙa wa manoma tare da samun damar noma adadin kayan abinci da makamantansu mai yawa wajen cimma muradun da gwamnati ta ƙudurta a fannin samar da isasshen kayan abinci da waɗanda kamfanonin cikin gida da waje ke buƙata wajen ci gaban tattalin arziki.

Bugu da ƙari, a tsarin da gwamnati ta ƙudurta dangane da ƙungiyar NECAS shi ne a baiwa manoma rancen kayan noma (taki da motoci da ingantaccen iri) ga manoma domin wadata ƙasa da isasshen kayan abinci, wanda bayan girbe amfanin gona su dawo da bashin, tare da sake mayar da shi ga wasu manoman da nufin ya ɗore. Haka al’amarin yake dangane da sabon shirin gwamnatin tarayya wajen baiwa ƙungiyar manoma shinkafa ta RIFAN alhakin shiga tsakanin gwamnati da manoma a shirinta na bunƙasa noman shinkafa a Nijeriya.

Duka waɗannan tsare-tsaren ɗaruruwan biliyoyin naira da gwamnatin tarayya ta fitar, ba su kai bantensu ba, saboda yadda suka gamu da manya-manyan kurakurai kala-kala, waɗanda suka haɗa da rashin ƙwararrun mutane masu amana, waɗanda za su aiwatar da tsarin zuwa ga manufar da aka tsara shi.

Saboda ta hanyar ƙwararru ne kaɗai za a bi wajen zaƙulo manoma na gaskiya, wanda suka ɗauki harkar noma sana’a, kuma daɗaɗɗu a fagen, masu kishin da za su bayar da gudunmawa wajen goya wasu ƙanana a bayansu don nona musu hanyar da zata taimaki gwamnati cimma wannan burin da ta saka a gaba.

Wannan babban givin ne ya jawo wasu maras kishi da bara-gurbin yan siyasa suka yiwa shirin mummunan targaɗen da ya kasa kai wa zangon da aka tsara zai isa. A sa’ilin da gwamnatin tarayya ta ware waɗannan maƙudan kuɗaɗe, a matsayin tallafa wa harkokin noma, tare da kyakkyawar manufa, amma ba tare da bibiyar yadda tsare-tsaren suke gudana ba, hakan ya bai wa maras kishi ƙasa da ci gaban al’umma damar watanda da dukiyar yan ƙasa- rijiya ta bayar guga ta hana.

A wani sabon yunƙurinta na tunkarar matsalar ƙarancin abinci, hauhawar farashin kayayyakin abinci da na masarufi, samar da ayyukan yi ga yan ƙasa, a wani mataki na ɗaukin gaggawa, gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahamed Tinubu, ma’aikatar kula da ayyukan noma da samar da abinci, a makon da ya gabata ta ƙaddamar da baiwa manoma tallafin noman alkama na rani, na bana (2023/2024) a ƙarƙashin shirin bunƙasa noma na National Agricultural Growth Scheme and Agro Pocket (NAGS-AP), wanda ake sa ran noma ton 1,250,000 na alkama a kowace shekara. Kuma bisa ga ƙididdigar masana, idan shirin ya gudana kamar yadda aka tsara shi, zai taimaka wajen rage hauhawar farashin kayayyakin abinci, samar da aikin yi, inganta habyoyin dogaro da kai tare da haɓaka tattalin arziki.

Da yake jawabi a lokacin ƙaddamar da shirin a ƙauyen Kadume dake ƙaramar hukumar Hadejia a jihar Jigawa, Minista a Ma’aikatar Noma ta Nijeriya, Sanata Abubakar Kyari ya ce: “A wani vangare na shirin gwamnatin tarayya wajen tallafawa kimanin manoma 150,000 zuwa 250,000 na kashi 50 cikin ɗari domin samun damar noma tsakanin kadada (hekta) 200,000 zuwa 250,000 wajen cimma ƙudurin ta na tan 1,250,000 na alkama.”

Ministan ya ƙara da bayyana cewa, wannan shiri na noman rani wani muhimmin vangare ne na yunƙurin bunƙasa noma a ƙarƙashin shirin: AgroPocket (NAGS-AP), wanda aka samar da shi ta hanyar ranto dalar Amurka miliyan 134, tare da haɗi da Bankin Raya Afirka (AfDB) a Nijeriya. Ya ce babban ƙudurin wannan Gwamnati shi ne farfaɗo da harkokin noman shinkafa, masara, rogo da alkama, a ƙasar nan.

Har wala yau, akwai yuwar Gwamnatin Tarayya ta faɗaɗa adadin yawan ƙananan manoman zuwa sama da 42,000 tare da baiwa kowane manomi ɗaya tallafin kayan noma kashi 50 cikin ɗari daga adadin kuɗin da gwamnatin ta kashe wanda aka ƙiyasta kashe naira 361,000 ga kowace kadada ɗaya.

A hannu guda kuma, Ministan Ma’aikatar gona, Sen. Abubakar Kyari ya gargaɗi waɗanda suka ci gajiyar tallafin da cewa kada su kuskura su sayar dasu, sannan da kashedi mai zafi dangane da karkatar da kayan, ya ce wajibi ne su yi amfani dasu ta hanyar da ta dace na gudanar da aikin noman alkama.

Haka zalika kuma, ya ja kunnen manoman da cewa su tanadi wannan tallafin domin ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu tare da cikkar buri da ƙudurin Gwamnatin Tarayya na kawo wa talaka sauƙin rayuwa ta fuskar bunƙasa aikin noma don samar da isasshen abinci.

“Za mu ɗauki matakan bin diddigin ku tun daga ranar da kuka shuka irin alkamar har zuwa lokacin girbi, za mu zuba ido mu ga kyakkyawan sakamakon amfanin gonar da zaku cika kasuwanni dashi.” In ji shi.

A hannu guda kuma, Ministan ya baiwa jami’an tsaron Al’ummar Nijeriya ta Jan-wuya (NSCDC) tare da haɗi da sauran jami’an tsaro su sanya ido sosai wajen daqile duk wani yunqurin karkatar da kayan, saɓanin yadda aka tsara aiwatar da su.

Blueprint Manhaja ta jiwo ra’ayoyin wasu daga cikin manoma a jihar Yobe dangane da raba wannan tallafin noman alkama, inda kaso mai yawa suka bayyana rashin gamsuwarsu dangane da yadda gwamnatin ta raba wannan tallafin.

Alhaji Ishaq Muhammad, manomi a garin Gashu’a ta qaramar hukumar Bade, ya ce bashi da masaniya kan raba wannan tallafin noman alkama, ya kada baki ya ce, “Da kimanin ƙarfe 8:00 na dare na ga saƙon kar ta kwana ya shigo wayata (ban san wanda ya bayar da lambar wayata ba) sai daga baya wani mutum (ya ɓoye sunan shi) ya kira ni, ya ce an tura maka saƙon kayan noman alkama, gobe da safe ka tafi Filin Agric. Katuzu. Bayan na zo aka ce na je na nuna saqon, daga baya mutumin ya karɓi kayan, ya bani naira 25,000.”

Wakilinmu ya gano cewa, kowane manomi zai biya naira 180,000 sannan a bashi buhu 7 na takin zamani samfurin (NPK Nagari), lita 7 na takin zamani na ruwa, tare da magudanun kashe ciyawa da ƙwari 4, sai buhun irin alkama (50kg) guda biyu. Sannan kimanin kaso 70 cikin ɗari na waɗanda aka turawa saƙon karɓar kayan, manoma bogi ne, yayin da wasu daga cikin su ƙananan yara ne da basu zarta shekara 12 zuwa 17 ba.

Haka zalika, manoma da dama sun koka dangane da yadda waɗanda aka ɗorawa alhakin raba kayan basu yi amfani da alƙaluman manoman bogi wajen zaƙulo mutanen da suka ci gajiyar tallafin, savanin manoma na gaskiya. Kamar yadda Mallam Usman Abubakar, manomi a ƙauyen Azam na ƙaramar hukumar Bade ya koka da cewa, “Idan zancen gaskiya za a yi, mune manoman alkama, wanda na kwashe sama da shekara 20 Ina noman alkama. Amma bamu da masaniyar raba tallafin sai ranar da ake aiwatar dashi, ka ga kenan bakin alƙalami ya bushe.”

Alhaji Jaɓɓi Mai-kanwa Gashu’a, shi ne Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar manoma ta jihar Yobe, ya bayyana cewa, “Ni ma haka na tsinci labarin ana raba kayan tallafin noman alkama a nan jihar Yobe; babu wanda ya tuntuɓe mu a matsayinmu na shugabannin manoma- walau Gwamnatin Tarayya ko ta jihar Yobe kan batun. Amma iya fahimtarmu, ƙila al’amari ne wanda yan siyasa suka yi babakere a ciki.

“Amma idan manoman gaskiya gwamnati take nema, ya dace a tuntuvemu, saboda muna cikin wannan sabga ta noma sama da shekara 70. Duk da bamu yi mamaki ba, amma abu ne mai wahala Gwamnatin Tarayya ta cimma burinta a wannan aiki,” ya bayyana.

Har wala yau, wakilinmu a jihar Yobe ya tuntuvi ɗaya daga cikin masu hannu wajen aiwatar da raba kayan tallafin noman alkama, Alhaji Ɗayyabu Gashu’a, ta wayar tafi-da-gidanka inda ya ce ba zai ce komai ba kan batun.