Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya sanya hannu a kasafin kuɗi na shekara 2024. Sai da majalisar dokoki ta jihar ta shafe kwanaki talatin da uku tana ta tafka muhawara akai tare da gayyato kwamishinoni da shugabannin ma’aikatu kafin su amince da zartas da kasafin kuɗin.
Gwamnan da ya sanya hannu a kasafi kuɗin a gaban babban joji na jiha mai shari’a Musa Danladi da Alƙalin Alƙalai Dr kabir Abubakar.
Sauran sun haɗa da ‘yan majalisar dokoki na jiha da ‘yan majalisar zartaswa ta jiha da kuma manyan jami’an gwamnatin jihar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya yaba wa ‘yan majalisar dokoki na jihar a bisa namijin ƙoƙari da suka yi wajen amincewa da kasafin kuɗin a cikin ƙanƙanin lokaci.
Ya kuma jinjina wa ‘yan majalisar wajen zartas da ƙudurori har guda goma cikin ƙanƙanin lokaci.
Malam Dikko Raɗɗa ya yi kira ga ‘yan majilisar da su ci gaba da haɗa kai da gwamnatinsa don samar da ababen more rayuwa a jihar.
Gwamnan ya ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta bi ƙa’idojin da bin kwa-kwaf wajen zartas da buƙatuwa al’umma da kuma kamanta gaskiya da riƙon amana wajen sarrafa dukiyar jihar.
Ya kuma sanar da cewa harkokin tsaro ya inganta a jihar da kashi sittin bisa ɗari wanda ya ce abin a yaba ne tare da godiya ga Allah.
