Rahoton Tattalin Arzikin Afirka na 2023 ya nuna buƙatar gyaran fuska a nahiyar don samun ci gaba mai ɗorewa

Rahoton Tattalin Arziki na Afirka 2023 (ERA 2023) ya bayyana cewa, akwai buƙatar yin ƙwarya-ƙwaryan gyaran fuska domin samun ci gaba mai ɗorewa da kuma jajircewa don cimma nasarar da ake fatan gani.

Har ila yau, rahoton ya ce: “Manufofin masana’antun da suka bunƙasa na buƙatar mayar da hankali ga sassan biyu da kuma samun daidaitattun abubuwa na yau da kullum. Sannan yana da mahimmanci ƙasashen yankin su gano ingantattun hanyoyin haɗin kai da dabarun aiwatar da manufofin ci gaba don haɓaka harkokin masana’antu.”

Rahoton mai taken: “Gina gurbin Afirka da ya dace wajen bunkasa tattalin arzikin duniya”, wanda Darakta mai kula da harkokin tattalin arziki da mulki a hukumar kula da tattalin arzikin Afirka ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNECA), Adam Elhiraika, ya gabatar a Abuja ranar Litinin, ya nuna cewa, tsarin ci gaban tattalin arzikin duniya a halin yanzu yana ba da mamaki ga ƙasashen Afirka bisa yadda suke da buƙatar hanzarta habaka masana’antu ta hanyar yin gwaji da kyau kan abin da zai fi zama mafita gare su da kuma yadda za su daidaita lamarin bisa tsarinsu na gida.

Elhiraika ya bayyana cewa, ci gaban da ake samu a Afirka yana da alaƙa da fitar da kayayyaki, yin aiki da manya kasashen duniya da kamfanoni, da bin ƙa’idoji da kuma haɓaka ƙungiyoyin masana’antu.

Waɗannan abubuwa, bisa ga rahoton na ERA 2023, ana buƙatarsu a ɓangarori daban-daban ta fuskar ire-iren kamfanonin da ake da su da kuma ƙarfin fasaharsu.

A nashi ɓangaren, Babban Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya a Nijeriya, Mista Matthias Schmale, wanda Masanin Tattalin Arziki, Nonso Obikili, ya wakilta, ya lura cewa abubuwa marasa daɗi daban-daban, kamar illolin da annobar COVID-19 ta haifar, da yunƙurin mamayar da Rasha ke yi a Ukraine, da sauyin yanayi ya sa Afirka ta fuskanci koma-baya wajen cimma muradun ci gaba mai ɗorewa na duniya (SDGs).

Ya ba da misali da yadda talauci a cikin 2021 ya ƙaru sosai, lokacin da kusan ‘yan Afirka miliyan 30 suka faɗa ƙangin matsanancin talauci, inda hakan ya haifar da asarar ayyuka miliyan 22.

“Ƙasashe goma da suke da mafi yawan matalauta sun kai kashi 64.7% na nahiyar. Ƙasashe huɗu na farko—Nijeriya (miliyan 100), Jamhuriyar Demokurafiyyar Congo (miliyan 67), Tanzaniya (miliyan 36), da Habasha (miliyan 33)—sun ɗauki kashi 42% na talakawa da kef ama da talauci.” In ji Schmale.

Don haka, ERA 2023 ya yi kira da a samar da sabbin dabaru ga ƙasashen Afirka don magance ƙalubalen matsalar tattalin arzikin duniya. Rahoton ya yi kira da a inganta yadda ake magance matsaloli da samar da jajircewa ta hanyar tsare-tsare masu kyau na ci gaban kasa da shugabanci nagari, da kuma kawo sauyi ga tsarin ci gaban masana’antu.

Bugu da ƙari, Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Dokta Tope Fasua, ya bayyana koma-bayan tattalin arzikin da Nijeriya ta samu tun a shekarun baya da suka haɗa da: hauhuwar farashin kayayyaki a farkon shekarun 1970 bayan tashin gwauron zabon farashin mai a shekarar 1973; koma bayan shekarun 1980 saboda faɗuwar farashin kayayyaki; da kuma wani matsalar da aka samu a tsakiyar shekarun 2000 sakamakon faɗuwar ɗanyen mai.

“Muna rayuwa cikin rashin daidaito ta fuskar tattalin arzikinmu, kuma yawancin Afirka har yanzu suna fama da irin wannan matsalar.” In ji shi.

Daga cikin wadanda suka halarci taron gabatar da rahoton akwai wakilan ofishin jakadancin Amurka, Tarayyar Turai, Sashen Bunƙasa Ci Gaba na USAID, Ma’aikatar Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki ta Tarayya, Ma’aikatar Kuɗi, Babban Bankin Nijeriya da kuma hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya.