Ɗan APC da ɗan PDP Ɗanjuma da Ɗanjummai ne – Sule Lamiɗo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma jigo a Jam’iyyar PDP ya ce zargin da tsohon shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC Chief Bisi Akande ya yi cewa idan PDP ta dawo mulki ‘yan Nijeriya za su sake shiga qunci ba gaskiya ba ne.

Alhaji Sule Lamido ya ce duk dan APCn da yake ganin PDP ce ta lalata Nijeriya to da shi a ciki, kasancewar shi ma asali dan PDP ne.

Sule Lamido ya ce ya yi mamakin kalaman Bisi Akande kan cewa PDP musiba ce, annobar bala’i ce azaba ce, amma duk da hakan ayi masa afuwa saboda tsoho ne.

Ya qara da cewa; “Amma kar ya manta kuma ‘yan Nijeriya kar su manta zabukan da aka yi a Nijeriya na shekarun 1999 da 2003 da 2007 da 2011 kuri’un PDP kadai sun fi na dukkan jam’iyyu.

Saboda haka, duk dabarar mai dabara, duk wayon mai wayo, sai da aka samu mutanen PDP, da Olusegun Obasanjo a lokacin suna fada da Goodluck Jonathan, da su Bukola Saraki, Atiku da Abdullahi Adamu da Aminu Waziri Tambuwal da sauran gwamnonin PDPn , suka marawa APC baya aka haifi ainahin gwamnatin Buhari.

“Abin da Bisi ya manta shi ne gwamnatin Buhari ‘yar haramun din PDP ce, yar PDP ce amma ta haramtacciya.”

Kan batun da Bisi Akande ya yi cewa dan takarar shugaban kasa karkashin jam’yyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, na jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da na jam’iyyar Labour Peter Obi na yunqurin hadewa domin PDP ta sake dawowa kan mulki domin sake jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali.

Sai Sule Lamido ya qara cewa: “Ai mantawa ya yi cewa sai da aka yi irin yunkurin na hadewa sannan suka samar da APC kuma duk da ana ganin mu annoba da azaba ne.

Amma aka haifi ‘yar waliyya wato jam’iyyar APC amma gaskiyar magana ita ce jam’iyyar APC ‘yar haramun din PDP ce. Saboda ita mace ce da bata haihuwa, sai ‘’yan PDP suka taimaka ma ta akai ciki, don haka gwamnatin Buhari ‘’yar PDP.”

A karshe Sule Lamido ya ce abin da Bisi ya yi babu laifi, zai iya mantuwa amma ‘yan Nijeriya su yi nazari da mulkin PDP da na APC. Shin a yanzu a Nijeriyar an fi arziki, ko zumunci ko walwala? A mulkin Buhari na shekara takwas kuma a Arewa, an gagara kammala hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wasu dai na ganin tun da jam’iyyar PDP ta rasa mulki, ta gagara taka rawar da ya dace a matsayin ‘yar hammaya domin dawowa karbar iko.

Sai dai Sule Lamidon ya ce duka manyan ‘yan jam’iyyar APC dukka ‘yan PDP ne, “hannun dama ne yake fada da hannun hagu, duk wanda za ka zaga kan ka za ka yi wa”.

“In zagi Abdullahi Adamu, ko Amechi, ko Wamako, ko Saraki, ko Kwankwaso, Ganduje.’’