Daina biyan kuɗin fansa shi zai kawo ƙarshen garkuwa da mutane — Ministan Tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya ce lokaci ya yi da za a daina biyan kudin kansa saboda haka ne kadai hanyar kawo karshen masu garkuwa da mutane.

Ministan ya bayyana haka ne a taron majalisar zartaswa ta kasa da aka gudanar a ranar Laraba.

Ya ce Shugaban Kasa ya bai wa dukkan hafsoshin tsaro goyon baya da ta kamata don ganin an kawo karshen garkuwa da mutane da ya yi kamari a kasar.

Ministan tsaron ya ce dokar Nijeriya ta hana bayar da kudin fansa kuma bai kamata mutane su rika biyan kudi ba saboda ba shi da amfani.

“Babbar matsalar ita ce yadda mutane ke fitowa a kafafen yada labarai suna neman taimako, har a zo a tara domin biyan fansa. Hakan bai dace ba.

“Idan muka daina biyan kudin fansa, sannu a hankali ayyukan masu garkuwa da mutane zai zama tarihi,” in ji Badaru.

Dangane da yadda rashin tsaro ke kara ta’azzara a Abuja, babban birnin kasar da kuma garkuwa da mutane da ake yi a yankunan gefen birnin, Ministan ya ce ayyukan da ake yi na korar ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya shi ya sa suke ta kaura da guje-guje.

“Shugaban kasa ya ba mu umarni tare da duka hafsoshin tsaro, ya kuma ce lallai a je a tsayar da wannan abu da ke faruwa. Kuma mun sa kaimi don ganin mun kawo karshensu,” in ji Badaru.

Ya ce ana ci gaba da fatattakar ‘yan bindigar a jihohin Zamfara da Borno don ganin an dakile ayyukansu.

By Editor