Daga AMINA YUSUF ALI
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shiraya don mayar da manyan sassansa zuwa jihar Legas. Wannan jawabi yana ƙunshe ne a cikin wata takardar yarjejeniyar cikin gida wacce aka ba wa majiyarmu damar samu.
Wannan yunkuri a cewar wani jami’in CBN ɗin wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, an yi ne domin a rage cinkoso a babbar shalkwatar bankin da ke Abuja.
Kodayake wasu daga cikin ma’aikatan na CBN ɗin sun yi tirjiya a kan komawa legas ɗin saboda suna ganin cewa wannan lamari an yi shi ne saboda qabilanci zalla ba don wani abu ba. Sai dai kuma majiyar tamu ta ce an yi shi ne don smaun bunƙasa da kuma tsaro.
Kuma a cewar sa, ma’aikatan da canjin wurin aikin ya shafa ma kalilan ne ba masu yawa ba. A cewar sa wasu sassa ne da suka hada da sashen bincike ne kadai suka kasance sun tabu da wannan canjin.
Don haka a cewar sa wannan hijirar sassan bankin kusan taimaka wa wadannan ma’aikata ta yi kuma ta rage yawan kudaden da za a kashe wajen bayar da tsaro.
Majiyarmu ta bayyana cewa, sassan CBN din da ake sa ran za a komar da su birnin na Ikko kamar yadda Gwamnan Babban Bankin, Yemi Cardoso ya bayyana sun hada da, Sashen sa ido a harkar banki, Sashen da ya shafi hulda da sauran ma’aikatu, Sashen kula da haqqin mai amfani da kaya, sashen sarrafa harkokin biyan kudi, da kuma sashen Tsara harkar kudi.
Sai dai a cewar Gwamnan Babban bankin ya ce da ma yawanci sassan bankin suna Legas wani zubin sukan tura ma’aikatansu daga abuja su yi wasu watanni suna aiki a Legas sannan su dawo shalkwatar da take a Legas.
A cewar sa suna sane da hadarurrukan da ake shiga a tafiye-tafiye a Nijeriya amma suna rokon ma’aikatansu da su kasance masu hakuri domin kusan wannan canjin wajen aikin ya kasance saboda amfanin kansu ne. Haka kuma an yi ne don kara bunkasa bankin ta kowacce fuska a cewar sa.
