Daga MAHDI M. MUHHAMMAD
Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da duk wani nau’i na cin hanci da rashawa ko rashin tausayi daga mambobin majalisarsa ko ma’aikatan gwamnati a jihar Zamfara ba.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa na musamman a zauren majalisar a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce majalisar ta kasance taron zartarwa na farko na gwamnatin Zamfara a shekarar 2024.
Ya qara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya bukaci dukkan masu rike da manyan muqamai da kwamishinoni da masu ba da shawara na musamman da su fahimci manufar sa tare da yin gyare-gyaren da suka dace.
Sanarwar gwamnan ta ce: Zuwa ga Kwamishinoninmu, Shugabannin Hukumomi da Ma’aikatunmu, ku ne Manyan Jami’an Gudanarwa a cikin gwamnati. Ba ku kadai ba ne masu gudanarwa. An nada ku don samar da jagoranci na gari ne, ba don bayar da kwangila ko raba kayan aiki cigaban kan ku ba.
“Ku ba ’yan kwangila ba ne; ku masu hidimta wa mutane ne. Dole ne ku cire tunanin cewa an nada ku don yin wani abu banda hidima da inganta rayuwa dimbin jama’a ta hanyar samar da kayan aiki da abubuwan more rayuwa da za su tallafa wa rayuwarsu da ayyukansu ba.
“Dole ne mu kawo canjin da ake buqata domin ciyar da jihar gaba; dole ne mu yi abubuwa iri daban.
“Ba mutanen jihar nan sun zabe mu ne don kawai mu maye gurbin fuskoki da halayen waxanda suka gabace mu ba. An zave mu ne don mu canja yadda ake gudanar da harkokin gwamnati.”
Gwamnan ya kara nanata wa majalisar cewa ba ya shiga cikin gwamnati ne don neman kudi ba.
“Game da haka, ina gaya muku wannan a yau: Ba zan yarda da duk wani aiki na cin hanci da rashawa da rashin tausayi daga kowane mai riqe da mukami ko ma’aikacin gwamnati ba. Na sha cewa ban zo nan don neman kudi ba, kuma duk wanda ke da burin arzuta kansa gara ya canja shawara ko kuma ya yi murabus daga gwamnati cikin mutunci.”
