‘Yadda ‘yan bindiga suka yi awon gaba da ‘yan mata tara a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wasu gungun ‘yan bindiga sun afka wa Unguwar Mareri dake cikin Gusau, babban Birnin Jihar Zamfara a daren ran Asabar inda suka yi awon gaba da ‘yan mata tara tare da wani maƙwabcinsu .

Rahotanni sun nuna cewar ‘yan bindigar da ɗauke da muggan makamai sun yi dirar mikiya a Unguwar sunata harbe-harbe kafin su samu nasarar sace ‘yan matan.

Hakazalika, wakilinmu ya tattaro cewar ‘yan matan da lamarin ya shafa ‘yan asalin garin Anka ne cikin Ƙaramar Hukumar Anka a jihar ta Zamfara.

Waɗanda abun ya rutsa da su sun haɗa da: Sanaratu Marafa, Halimatu Marafa, Rukayya Marafa, Sakina Yusuf Anka, Amina Yusuf Anka, Habsat Yusuf Anka, Fatima Sani Anka, Suwaiba Mareri, Aslam Jariri da kuma wani maƙwabcinsu.

Al’ummar yankin na Mareri sun daɗe suna fuskatar matsalar tsaro lamarin da ya tilast wa mafi akasarin mazauna Unguwar barin gidajensu don tsira daga hare-haren ‘yan bindigar.

Wasu mazauna Unguwar sun nuna alhininsu bisa yadda yankin ke fuskatar ƙalubalen hare-haren ta’addanci, suna masu yin kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin jihar da a ɗauki matakin da ya dace don inganta tsaro da lafiyarsu da kuma dukiyoyinsu.

Wani mazaunin yankin da buƙaci a sakaya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewar yankin da ke a cikin babban birnin Jihar ta Zamfara yana cikin wani halin ko-in-kula daga ɓangaren hukumomi dangane da matsalar tsaron da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.

“Muna fuskatar ƙalubalen hare-haren ‘yan bindiga kusan koyaushe amma babu wasu jami’an tsaro da aka ajiye a yankin don kare rayuwarmu,” in ji shi.

Daga nan, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar Zamfara da su kawo masu ɗauki ta fannin tsaro .

“Kowa ya san halin da ake ciki na tsananin rayuwa, ba za mu iya barin yankinmu da gidajenmu mu kama na haya ba, saboda haka muke kira ga Gwamnatin Tarayya da ta jihar Zamfara da a ɗauki matakin gaggawa don kare rayuwarmu.”

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, ƙoƙarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Asp. Yazid Abubakar kan batun ya ci tura.