‘Yan bindiga sun kashe jigon APC a Filato

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga a Jihar Filato sun bindige kakin Jam’iyyar APC a jihar, Sylvanus Namang.

Lamarin ya faru ne a garin Pankshin da ke yankin Ƙaramar Hukumar Pankshin a jihar.

Majiya ta kusa da APC a jihar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta tabbatar da afkuwar lamarin. Tare da cewa, marigayin ya cika ne sabili da raunin da ya ji sakamakon harin da aka kai masa.

Haka nan, majiyar ta ce APC za ta fitar da bayani a hukumance dangane da badaƙalar da ke tattare da mutuwar Namang.

News Point Nigeria ta rawaito cewa, an harbe marigayin ne a wajen ɗaki a otel ɗin da ya yi masauki da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

Bayanai sun nuna marigayin ya bar gida ranar Asabar da nufin halartar jana’iza a Pankshin inda a can ya gamu da ajalinsa.

Ya zuwa haɗa wannan rahoto, ba a samu jin ta bakin Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Filato, Alfred Alabo ba, sakamakon wayarsa na kashe a lokacin da aka yi ƙoƙarin jin ta bakinsa kan batun.