Tsadar rayuwa: Mata a dinga yi wa maza uzuri

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Allah Ya albarkace zuri’armu.

A yau dai shafin iyali zai yi jan kunne ne zuwa ga mata, ko in ce rarashi, kasancewar abinda za mu yi magana kansa haƙƙinsu ne a ba su, kuma daidai ne idan sun yi bori yayin da aka hane su. Sai dai masu azancin magana na cewa, “ɗaurowa take a ɗaure alƙali.” Yanayi da muka samu kanmu a yanzu ne abin duba ga kowacce mace mai hankali kafin ta zargi mijinta da rashin wadata da haƙoƙin da ya rataya kansa.

Halin da muka samu kanmu a yanzu sai dai hamdalla. A kullum matsin rayuwa sai ƙara ta’azzara yake. Hauhawan farashin kayan masarufi ya zama ɗan gida. Abin tashin hankali kuwa kaso mai yawa na jama’ar da ke fama da wannan matsin rayuwa samun su bai ƙaru ba.

Ya ke matar gida, kafin ki ɗaga murya zuwa ga maigidanki don bai kawo abin buƙata ba, ko bai kawo da yawa ba, ki fara da tambayar kanki, me yake samu a aiki ko kasuwancin da yake yi? Ko akwai wani ƙari da yake samu a wannan lokacin? Idan kuwa ki ka tabbatar da ba bambanci kan samun sa na da da yanzu, sai ki koma kan lissafin ababen da yake siyowa, kudinsu na da da kuma na yanzu.

Ina da tabbacin idan kin yi shi daidai za ki tarar kuɗin da ke kammala dukka buƙatunku a baya, ba za su iya bada kaso arba’in ba a yanzu. Idan haka ne, ina ki ke son ragowar sitin ɗin ta fito?

Ya ke matar gida, ki sani, ba mijinki ne kawai aka jarrabta ba yayin da matsin rayuwa ya yawaita, domin shi an jarrabce shi ne da siya da tsada, ke kuwa yin haƙuri da kaɗan ko rashi idan bai samu ba.

A ‘yan kwanakin nan mata da dama sun murje idonsu, sun sa masu toka, sun rufe kunne da ido daga gani da jin gaskiya, duk da cewa gata nan a gabansu. Wallahi idan ka ji wasu matan na zancen irin tayar da hankalin da suke wa mazajensu kan rashin kawo ababen buƙata sai kunya ta rufe ka. Wasu fa ko ragi aka samu ba za su lamunta ba, bare an zo babu.

Wannan ɗabi’a ta wasu matan na daga ababen da ke tadawa maza hankali daga hauhawan farashi, wallahi wani ba tashin kaya ne yafi tada masa da hankali ba, domin don ta tasa zai iya maneji, tsabar tashin hankali da za a girka a gidansa ne babban ƙalubale gare sa.

Ya ke matar gida, ki sani, a lokacin da ki ke wa mijinki tijara kan bai cike wasu daga ɗawainiyarku ba, ko bai yi ba ma gabaɗaya, to fa ba da shi ki ke faɗa ba, da wanda ya jarrabe shi da rashin abinda zai iya isar ku ne ki ke ja, domin shi bai isa ya ba wa kansa abinda Allah bai ba shi ba.

Duk da na san wasu za su iya kafa hujja da cewa, mazan ba su son ɗauke nauyin nasu yadda ya kamata, na san akwai wannan matsalar musamman a Ƙasar Hausa, sai dai a halin da ake ciki yanzu, kaso da yawa na mazan babu ce ke sa su hana ku ko su ba ku kaɗan. Don haka ko bisa ƙarya mijinki ya ce babu a irin wannan yanayi ki yarda da shi, ki yi haƙuri, wallahi za ki ga sakayya mai girma.

Ku ji tsoron Allah mata! Ku yarda da ƙaddara, ku amshi jarrabawar da Allah ke mana da hannu biyu, sannan ku yi addu’a Allah Ya kawo mana sauqi. Lallai Allah Mai jin addu’ar bayinSa ne, musamman masu haƙuri.