Ko motsa jiki na rage ƙiba?

Daga AISHA ASAS

Daga farko dai me ke jawo ƙiba mai yawa a jikin ɗan adam? Idan ka bi bayanan masana kan ƙiba a hankali za ka tarar da cewa, ƙiba mai yawa na samuwa ne sakamakon wasu ɗabi’u da jiki ba ya buƙata, na daga ababen da ake ce da wanda ke ba wa jiki fiye da abinda yake buƙata, kamar vangaren matsƙi da ke haifar da yawaitar kitse a jikin ɗan Adam idan ya yi yawa, ko kuma vangaren abinci mai zaƙi idan ya yawaita, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki wanda lokuta da dama shi ne limamin da ke jan ragamar mummunar ƙiba a jikin ɗan Adama. Domin da motsa jiki za ka iya ƙone kitsen da jiki ba ya buƙata.

Da yawa daga cikin waɗanda ke da qibar wuce wuri za ka same su da ɗabi’ar rashin son motsa jiki, da kuma cin abinci a kwanta. Wannan ɗabi’a ta hana abinci damar narkewa tare da karkasa shi zuwa kowanne muhalli ba ƙaramin taka rawa ta ke ba wurin samar da ƙiba ko tumbi.

Da yawa suna ganin cin abinci a kwanta ba komai ba, kuma a cikinsu ne aka fi samun masu ƙorafin ƙiba ta yi masu yawa ko ba su san me ke kawo masu ƙiba ko tumbi ba.

Idan mun fahimci wannan bayanin sosai, za mu gane rashin atisaye bayan cin abinci kawai zai iya zama silar samuwar ƙibar da ba a buƙata. Ba wai cin a kwanta ne matsalar ba, rashin motsa jikin wanda zai taimaka wa abincin ya samu narkewa kan lokaci.

Idan mun koma ɓangaren illar da ƙiba ta wuce wuri ke haifarwa jiki kuwa za mu fahimci daurewa ana motsa jiki bah ala ba ne idan an yi la’akari da wahalar da ke tattare da curutan da ƙiba ke haifarwa.

Na sani a wannan zamani da ƙiba ta zama ƙawa ga mata, zai yi wuya wasu matan su yarda tana da illa, duba da cewa da kuɗinsu suke siyo ababen da za su sha don su yi ƙiba, waɗanda akasarinsu ma suna da nasu lahanin da za su iya yiwa jikin.