Za a kafa Babban Bankin Afirka a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa, a shirye Nijeriya take ta karɓi Babban Bankin Afirka bisa la’akari da ƙudirin birnin tarayya, Abuja.

Tinubu ya yi wannan furuci ne sa’ilin da yake jawabi a wajen taron Ƙungiyar Ƙasashen Afirka (AU) da ke gudana a Addis Ababa, babban birnin ƙasar Habasha.

Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta tattauna da dukkan waɗanda suka dace domin tabbatar da bankin ya fara aiki ya zuwa 2028 kamar yadda aka shirya.

Shugaba Tinubu ya faɗa wa taron cewa, iya magance ƙalibalan Afirka na tattare ne da irin matsayar da shugabannin nahiyar suka cimma da kuma tabbatar da haɗin wajen magance matsalolin da ake fuskanta da guje wa ƙirƙirar sabbin matsaloli.

“Da daman matsalolin da muke fuskanta, kamar sauyin yanayi, rashin daidaito a kasuwanci ba yinmu ba ne.

“Amma kuma al’amurra irin juyin mulki da mulkin kama karya da yi wa wa’adin mulki da dokar ƙasa ta ayyana karan tsaye, su ne abubuwan da ke hana mu ‘yan Afirka cigaba,” in ji Tinubu a cikin wata sanarwar da ta samu da hannun Mai Magana da Yawun Shugaban Ƙasa, Ajuri Ngilale.

Yadda za a inganta sha’anin tsaro da bunƙasa tattalin arzikin nahiyar, na daga cikin batutuwan da shugabannin Afirka suka tattauna a wajen taron AU karo na 37.