Tambuwal ya bayyana a gaban Kwamitin Bincike

Daga BASHIR ISAH

A ranar Asabar tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal, ya bayyana a gaban Kwamitin Bincike mai bincike kan wasu ayyuka da gwamnatisa ta aiwatar a zamanin mulkinsa.

Gwamnan Jihar, Ahmed Sokoto ne ya kafa kwamitin domin bincike kan yadda harkokin gwamnatin da ya gada suka gudana.

Tambuwal ya isa gaban kwamitin ne tare da wasu muƙarrabansa, kuma rashin ba da shaidarsa ya sa kwamitin ya buƙace shi da ya sake dawowa ya zuwa wata ranar da za a sanar nan gaba.

Sanata mai wakiltar Sakkwato ta Kudu ya wallafa a shafinsa na sohiyal midiya cewa, “Yau na bayyana a gaban kwamitin bincike ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mu’azu Abdulkadir Pindiga wanda Mai Girma Ahmad Aliyu Sokoto ya kafa.

“Na samu rakiyar tawagar lauyoyina da wasu jami’ai a gwamnatina da suka haɗa tsohon SSG, Muhammad Mainasara Ahmad, tsohon Shugabam Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Muktar Magori, tsohon Babban Lauyan jihar kuma kwamishinan Shari’a, Dr. Sulaiman Usman, SAN, among da sauransu.”

Ya nuna cewa, bin doka abu ne da ya kamace kowane ɗan ƙasa, kuma babu wanda ya fi ƙarfin biyayya ga doka komai matsayinsa.

“Ina yi wa Kwamitin fatan nasara a ayyukansa,” in ji shi.