‘Yan bindiga sun kashe mutum tara, sun yi awon gaba da tsohon Daraktan CBN a Kaduna

Daga BASHIR ISAH

‘Yan bindiga sun kashe mutum tara a mabambantan hare-hare da suka kai a yankunan ƙananan hukumomin Kauru da Igabi a Jihar Kaduna.

Haka nan, sun yi garkuwa da mutum 35 ciki har da wani tsohon Daraka a Babban Bankin Nijeriya (CBN) haɗa da wani ƙanensa da matarsa.

Sai kuma wasu mutum tara da suka tagayyara sakamakon hare-haren.

A ranar Juma’a ‘yan bindiga suka kai hari ƙauyen Kwasam cikin yankin Ƙaramar Hukumar Kauru da misalin karfe 10 na dare inda suka firgita mazaun yankin da harbin bindiga.

Bayanai sun ce, maharan sun yi amfani da wasu daga cikin waɗanda suka kaman ne wajen gano gidan tsohon ma’aikacin CBN ɗin da suka yi garkuwa da shi.

Majiya ta ce wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun cimma ajali ne bayan da suka yi ƙoƙarin kuɓutar da waɗanda ‘yan bindigar suka tattara tun farko.

Majiyar ta ƙara da cewa, waɗanda suka riga mu gidan gaskiya yayin harin, sun haɗa da Danmasanin Gwaska, Mrs. Giwa John; Kapishi Barmu; Ganya Ubangida; Shigama Salisu da Gani Magawata da dauransu.

Yayin da waɗanda aka yi awon gaba da su kuwa, akwai Mr. Zakariya Markus kuma tsohon ma’aikacin CBN, Mr. Monday Markus, Mrs. Monday Markus, Mr. Alhamdu Makeri, Baban Fati na Kauru da sauransu.

Bugu da ƙari, mutum uku aka rawaito sun mutu a harin Igabi da ya auku a Gundumar Sabon Birni Ward, sannan an yi awon gaba da mutum 30.

Tuni dai Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya buƙaci sojoji a jihar da su fito su yi maganin ‘yan bindigar da suka kai hare-haren wanda yi sanadiyar salwantar rayuka da kuma garkuwa da mutane.

Gwamna Sani ya yi wannan kira ne ta hannun Kwamishinan Harkokin Tsaron Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, yayin ziyarar da ya kai ƙauyukan Gwada da Kerawa a Ƙaramar Hukumar Igabi.