Yadda Kakakin majalisar Bauchi ya koma muƙaminsa bayan yin murabus  

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Tsohon Kakakin Majalisar Dokoki Jihar Bauchi wanda a zaɓen gama-gari na ranar 18 ga watan Maris ta shekarar da ta gabata 2023 ya tsaya takarar zaɓen wa’adin wakilci zango na biyu, amma ya faɗi zaɓen, a ranar Laraba ya sake ɗare wa kujerar da ta shugabancin majalisar, sakamakon zaɓen cike gurbi da hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta yi a ranar 3 ga watan Fabrairu da ya gabata. 

Ɗan takarar shiga majalisar dokoki na jam’iyyar APC daga mazaɓar Ningi ta Tsakiya, Malam Khalid Ningi, shine ya ƙalubalancin zaɓen na tsohon kakakin majalisa Abubakar Yakubu Suleiman wanda aka gudanar a ranar 18 ga Maris na shekarar da ta gabata, 2023, lamarin da ya jaddada Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke zaɓen na mazaɓar Ningi, kana ta yi umarnin gudanar da zaɓen cike gurbi a mazaɓar da ta kai kakakin zuwa majalisa.

Zaɓen takarar kujeru huɗu ne na majalisar dokokin ta jihar Bauchi da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta gudanar da zaɓen cike gurbi a ranar Asabar 3 ga Fabrairu, 2024, biyo bayan umarnin Kotun ɗaukaka Ƙara, waɗanda suka ƙunshi mazaɓun Zungur/Galambi, Ningi, Madara/Chinade, da kuma Bauchi ta Tsakiya wacce ta tuntsurar da muƙaddashin majalisar dokoki ta jiha, Jamilu Dahiru.

Dukkanin kujeru majalisar dokokin guda huɗu waɗanda kotu ta ayyana a gudanar da zaɓen cike gurbi akan su, jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓuɓɓukan, har da guda biyu daga cikinsu waɗanda a baya suka yi wancakali da kakakin majalisa da muƙaddashinsa.

Allah ya taimaki Honarabul Abubakar Yakubu Suleiman wanda ya wakilci mazavar Ningi ta Tsakiya da ya lashe zaɓen cike gurbi da yawan ƙuri’u 11, 785, inda ya tiƙar da abokin takarar sa na jam’iyyar APC, Khalid Ningi days samu kuri’u 10, 339, kowanne sai da aka haɗa masa da ƙuri’un sa na zaɓen gama-gari da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar bara, 2023.

A zaɓen cike gurbin na kujerar Bauchi ta tsakiya dai, jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen da Jamila Dahiru ya yi mata takara da kuri’u 45, 240, kujerar ɗa’a gabanin wannan zaɓe ta tuntsurar da shi yana muƙaddashin makamin majalisa, inda ya kayar da abokin takararsa na jam’iyyar APC, mai yawan ƙuri’u 42, 266.

Ragowar kujeru biyu ma da aka yi zaɓen cike gurbi, a mazaɓun Zungur/Galambi da Madara/Chinade, su ma jam’iyyar PDP ce ta lashe su ta hannayen ‘ya’yan yakarkarun ta Dokta Ala Ahmed mai ƙuri’u 13, 920 da ya wancakalar da Dantali Ali na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 9, 710; da mazavar Zungur/Galambi da Yusuf Ahmed ya lashe da kuri’u 2, 233, inda ya tiƙar da Ibrahim Yuguda mai ƙuri’u 1, 928.

A zaman na majalisar dokoki ta jihar Bauchi na ranar Laraba, Kakakin majalisar dake kan kujera, Honarabul Babayo Mohammed wanda ya fito daga mazaɓar Hardawa/Akuyam sai kwatsam ya sanar da sauka daga kan kujerar tasa da tsohon kakalin majalisar, Honarabul Abubakar Yakubu Suleiman ya ɗare.

Idan za a iya tunawa dai, Honarabul Babayo Mohammed, bayan da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta zartar da hukuncin soke zaven tsohon kakakin majalisar, kuma jim kaɗan bayan ɓalewar Babayo, ya kaɗa baki a wajen wani taron masu ruwa da tsaki, inda ya yi furucin zai iya sauka daga kujerar ta kakakin majalisa, matuƙar tsohon kakakin ya ci zaɓensa na cike gurbi da aka gudanar ranar 3 ga watan Fabrairu da ta gabata.

Kuma saukar Honarabul Babayo Mohammed ke da wuya, da kuma mayewar tsohon kakakin majalisar bisa gurbi, sai shi da muƙaddashin kamin makalisar, Honarabul Ahmed Abdullahi wanda ya fito daga mazaɓar Dass, shi ma ya tiƙar da kujerar tasa, lamarin da ya sanya aka sake zaɓen tsohon muƙaddashin kakakin majalisar, Honarabul Jamilu Dahiru, shi ma ya maye gurbi.

Kakaki da muƙaddashi masu murabus sun bayyana cewar, abin da ya faru, ya biyo bayan alƙawari ne da su ‘yan majalisa suka ƙudura a baya na cewar, idan Honarabul Abubakar Sulaimen da Honarabul Jamilu Darihu suka ci takarar su ta zaɓen cike gurbi, za’a mayar masu da kujerun su na lakaki da muƙaddashi, domin su cigaba da jagorancin majalisar ta dokoki a jihar Bauchi.

Hon. Abubakar Yakubu Sulaiman, wanda ya tsallake rijiya da baya, biyo bayan ɗaye wa kujerarsa haɗi da mataimakinsa Hon. Jamilu Dahiru sun gode wa takwarorin nasu bisa ya kamata da dattaku da suka nuna wajen dawo da su bisa jagorancin majalisar, su na masu shan alwashin cigaba da yin jagoranci nagari domin amfanin ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi.