Ahmed Musa ya dakatar da kwantiraginsa da Sivasspor ta Turkiyya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Rahotanni sun bayyana cewa kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa ya soke kwantiraginsa da ƙungiyar Sivasspor ta Turkiyya.

An kawo ƙarshen kwantiragin tsakanin Musa da Sivasspor ta hanyar yarjejeniya.

Ɗan wasan mai shekaru 31 ya ɗauki matakin ne bayan ƙungiyar ta kasa biyan albashin sa na watanni shida da suka gabata.

Ɗan wasan gaba ya riga ya fara aiki don komawa wani kulob a lokacin bazara.

Musa ya koma Sivasspor daga wata ƙungiyar Turkiyya Fatih Karagumruk a shekarar 2022.

Ya buga wasanni tara a ƙungiyar ba tare da samun nasarar zura ƙwallo ko ɗaya a raga ba.