Kuriga: Za mu ceto yaran da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya – Gwamna Sani

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya sha alwashin ceto ɗaliban firamaren da ‘yan fashin daji suka yi garkuwa da su a yankin Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a jihar.

Ya sha alwashin ne a ranar Alhamis sa’ilin da ya ziyarci yankin domin jajanta musu kan abin da ya faru.

Ya ce ba a tabbatar da haƙiƙanin adadin yaran da aka sacen ba, amma cewa gwamnati na aiki tare da hukumar makarantar da ma al’ummar yankin wajen gano yawan yaran da aka yi awon gaba da su ɗin.

Ya ƙara da cewa, “Za a kafa kwamitin tsaro a Kuriga mai ɗauke da mambobi daga sassan yankin haɗa da hukumomin tsaro da kuma Gwamnatin Jihar.

“Zan gabatar da ƙorafi mai ƙarfi ga Babban Hafsan Tsaro da na Sojoji domin samar da barikin sojoji a Kuriga don ƙarfafa tsaro a yankin,” in ji Sani.

Gwamnan ya ƙara da cewa, “Samar da ‘yan Sandan Jiha zai taimaka wajen samar rundunar ‘yan sanda a Kuriga waɗanda za a tsinto su daga sassan yankin, kuma masu fahimtar halin da yankin ke ciki.

“Cikin sauƙi za su haɗa bayanan sirri, haka nan za a ƙarfafa su a hukumance ta yadda za su riƙe bindiga.”